Hukumar PSC Ta Kare Kanta Kan Daukar Tubabbun 'Yan Daba Aiki a Jihar Kano
- Hukumar jin daɗin 'yan sanda ta ƙasa (PSC) ta kare matakin ɗaukar tubabbun 'yan daba aikin kurtu a jihar Kano
- Kakakin PSC na ƙasa, Ikechukwu Ani, ya ce 'yan daban da suka tuba aka ɗauke su aikin sun gane aikata laifi ba ya haifar da ɗa mai ido
- Ya ce an tura su yankunansu domin zasu fi iya zakulo masu aikata laifukan ta'addanci a lungu da saƙo
FCT Abuja - Hukumar kula da ayyukan 'yan sanda ta ƙasa (PSC), a ranar Alhamis, ta yi ƙarin haske kan ɗaukar, "tubabbun 'yan daba" aikin ɗan sanda a jihar Kano.
PSC ta yi bayanin cewa ta ɗauki matakin ɗaukar 'yan daban da suka tuba ne a wani ɓangaren yunƙurin jami'an yan sanda na kawo karshen aikata laifuka a lungu da saƙo na jihar Kano.
‘Yan Najeriya dai sun nuna rashin jin dadinsu tare da yin kira ga hukumomi da su rika sanya ido a lokacin daukar aikin 'yan sanda, Daily Trust ta ruwaito.
Hukumar PSC ta kare kanta
Amma da yake kare matakin a wata sanarwa da ya fitar a Abuja, kakakin PSC, Ikechukwu Ani, ya yi musun cewa an ɗauki tubabbun 'yan barandan aikin kurtun ɗan sanda saboda sun gane gaskiya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce tubabbun 'yan daban da aka ɗauka aikin ɗan sanda a matsayin kurata, wanda ya haddasa cece ku ce, sun fahimci aikata laifi ba abu ne mai kyau ba.
A cewar Ani, an ɗauke su aiki ne domin wanzar da zaman lafiya, ci gaban tattalin arziki da jihar Kano, inda ya kara da cewa sun samu isasshen horo kan harkokin 'yan sanda.
Da Ɗumi-Ɗumi: 'Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Hari Gidan Ɗan Majalisar Arewa, Sun Tafi da Matarsa da 'Ya'yansa
A rahoton jaridar Guardian, Kakakin PSC ya ƙara da cewa:
"Ya zama dole mu yi bayanin cewa maza da mata da aka dauka a matsayin kurata na musamman an tura su aiki a yankinsu inda za su fi dacewa su kamo masu aikata laifukan ta'addanci."
"Wasu daga cikin matasan da suka tuba a baya ana amfani da su a matsayin ’yan bangar siyasa, sun fahimci cewa aikata laifi ba inda zai kai ka, kuma sun ba da kansu don taimakawa wajen tsaftace jihar."
"Muna sane da cewa jami'ai na musamman da aka ɗauka a Kano sun samu isasshen horo kuma suna aiki a kananan hukumominsu a karkashin kulawar rundunar ‘yan sandan jihar.”
Kano: Yan Sanda Sun Kama Mutum 30 Kan Yunkurin ‘Tayar Da Tarzoma’ Yayin Auren Gata
A wani rahoton kuma Yan sanda sun cafke mutane 30 da ake zargin suna yunƙurin kawo cikas a bikin Auren gata da aka yi ranar Jumu'a a Kano.
Kwamishinan 'yan sandan jihar Kano, Mohammed Gumel, ya ce mutanen sun bayyana abin da ya kawo su wurin ɗaura aure.
Asali: Legit.ng