An Yaudari Mutane Da Tikitin Musulmi-Musulmi Da Wasu Abubuwa 6 Da Gumi Ya Fadi a Sabon Bidiyonsa
Fitacccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi, ya tayar da kura bayan ya saki wani sabon bidiyonsa inda ya yi wa gwamnatin shugaban kasa Ahmad Tinubu kaca-kaca.
Harma Shehin Malamin ya yi barazanar cewa idan har shugaban kasar ya yi wasa za su sanya kafar wando daya da shi kuma ba zai shugabanci kasar na shekaru takwas ba.
A wannan babin, Legit Hausa ta lissafo jerin abubuwan da Sheikh Gumi ya amayar a cikin faifan bidiyonsa wanda ya girgiza intanet.
1. Ministan Abuja shaidanin mutum ne
Shehin malamin ya bayyana ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike a matsayin shaidanin mutum.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana hakan ne sakamakon tarban ambasan Isra'ila a Najeriya da ministan ya yi a ofishinsa.
2. Ka cire Wike ko mu sa kafar wando daya da kai, Gumi ga Tinubu
Gumi ya yi kira ga shugaban kasa Bola Tinubu da ya sauke ministan babban birnin tarayya ko kuma su saka kafar wando daya da shi
A cewarsa, Wike na so ya mayar da Abuja kamar Tel-Aviv ta yadda mulki zai koma hannun yahudawa harma a hana irinsu masu gemu shiga babban birnin tarayyar.
3. An yaudare mu da tikitin Musulmi-Musulmi
Har wayau, Shehin Malamin ya bayyana wadanda suka tallata tikitin Musulmi-Musulmi a yayin babban zaben 2023 a matsayin munafukan banza.
Ya ce:
“Ina masu tikitin musulmi-musulmi, munafukan mutane, munafukan banza? Abuja ta koma Tel-Aviv.
"Ba ku ji sun yi tsit ba. Sun san abin da su ke yi. Daman take-take ne.”
4. Ana cutar yan arewa
Shehin malamin ya ce ana cutar yan arewa cuta irin na halaka. Ya ce da kasuwancin halal, babu yadda za a bari dan arewa ya yi biliyan daya.
Ya ce an mayar da yan arewa kamar kaji wadanda da zaran an watsa masu hatsi shikenan. Ya ce sai lokacin zabe ya yi a zo a raba masu taliya.
5. Idan aka ba kirista bindiga sai ya cutar da yan arewa
Gumi ya kuma ce bai kamata a bar tsaron kasar nan a hannun yan kudu da kirista ba domin da zaran sun samu bindiga burinsu shine cutar da yan arewa.
Ya ce:
"Akwai wani Rabaran a lokacin Buhari yake cewa Musulmai duk mun kwace kayan mulki da menene da manene, na ce eh mun kwace. Amma me? Hankalina na kwance domin na san shugaban soja ko shugaban nan ba zai zo ya yi kokarin kawo mun hari ba. Ko bai yi wani abu na kareni ba amma dai na san ba zai kawo mun hari ba. Kuma kaima kiristan da kake magana ka san ba za a yi amfani da su a cuce ku ba. Amma idan ka ba nasu mulki, ka basu bindiga su za su yi kokarin su cutarmu."
Har ya yi misali cewa yan kudu ne suka kashe Sardauna, Murtala Muhammad, Tafawa Balewa harma ya ce da kyar Babangida ya sha a hannunsu.
6. Idan Isra'ila ta shigo Najeriya sai an kashe duk wani malami, Gumi
Malamin ya kuma yi hasashen cewa idan har Isra'ila ta shigo kasar nan, sai an kashe duk wani malami.
Ya ce:
"Idan Isra'ila ta shigo kasar nan babu abun da za ta yi, aiki za ta yi duk wani malami da ake jin maganarsa sai sun kashe shi, mun ga alamunsu, me yasa suka kashe Jaafar? Allah ya ji kan shi. Me yasa suka kashe Albani? Ga shi nan suna kashewa.
Ai lis ne guda shida, tuntuni aka gaya mana tsaro. Shiyasa yan sandan dan, ba ku gani lokacin Buhari ma ina da yan sanda kuma ba na shiri da gwamnati? dole ne su bayar domin rahoto ya zo cewa kaima kana cikin jerin saboda haka muka nemi a ba mu yan sanda saboda kariya shiyasa suke ba mu.
Saboda haka ko shugaban kasa yana sona ko baya sona dole ya ba ni kariya yan sanda idan ba haka ba a rataya mai raina a wuyansa yake.
7. Dan siyasa dala ce a gaban shi
Gumi ya yi kira ga al'umma da su waye kada su zama wawaye domin dan siyasa dala ce a gabansa ba al'umma ba.
Ya ce:
"Ina fada maku wadannan ne don ku waye, kada ku zama wawayen mutane. Ku dunga wayewa, don dan siyasan can dala ce kawai yake so a ba shi, ya je hutu, ya je asibiti shikenan ya mace da al'umma."
“Ba Za a Yarda Da Haka Ba”: Shehu Sani Ya Yi Martani Yayin da Gumi Ya Kira Wike Da “Shaidanin Mutum”
A gefe guda, mun ji cewa tsohon sanata da ya wakilci Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya bayyana cewa ana iya caccakar ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, a matsayinsa na wanda ke rike da mukamin gwamnati amma ba wai kan addininsa ba.
Sani ya ce yana adawa da amfani da "addini mai guba" a kan tsohon gwamnan na jihar Ribas.
Asali: Legit.ng