Abu Ya Lalace a APC Bayan Dakatar da Shugaban Jam’iyya a Kan Zargin Yin Fyade
- Jam’iyyar APC ta dauki matakin soma ladabtar da wani shugabanta wanda ake zargi da laifin yi wa yarinyar gidansa fyade
- Yanzu haka Alhaji Saleh Idris ya na tsare bayan an kai karar shi gaban wata kotun majistare da ke birnin Dutsen jihar Jigawa
- Kafin a zarge shi da wannan danyen aiki, Saleh Idris ne shugaban jam’iyyar APC mai mulki na reshen karamar hukumar Roni
Jigawa - Shugabannin jam’iyyar APC na reshen jihar Jigawa sun dakatar da shugabansu na karamar hukumar Roni, Saleh Idris.
Ana zargin Alhaji Saleh Idris ne da zargin yi wa karamar yarinya mai shekara 14 fyade, wanda hakan ya kai ga samun juna biyu.
Punch ta ce wanda ake zargin an yi wa lalatar ‘yar aikin gidan jagoran jam’iyyar ta APC ne.
Jam'iyyar APC ta yi magana
Shugaban APC na jihar Jigawa, Aminu Sani Gumel ya fitar da jawabi dauke da sa hannunsa, ya mikawa manema labarai a makon nan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yanzu aka an tsare Saleh Idris bisa umarnin karamin kotun majistare da ke Dutse.
Lamarin ya kai kotu ne bayan jami’an rundunar NSCDC sun cafke shugaban jam’iyyar a ranar 4 ga watan Oktoba, aka kai shi kara.
Wani ‘danuwan yarinyar da ake cewa an yi wa fyaden ne ya kai maganar wajen hukuma.
NSCDC ta kama Shugaban APC
Daily Post ta ce mai magana da yawun bakin NSCDC na reshen jihar Jigawa, Adamu Shehu ya tabbatar da haka a wani jawabi da ya fitar.
Mista Adamu Shehu ya ce bayan yin gwaji a asibiti, an gano ‘yar aikin da ta kai kara ta na dauke da juna biyu na watanni hudu da rabi.
"Bayan zargin fyade da yi wa karamar yarinya ciki da kuma sakamakon binciken da reshen jiha na jam’iyya ta fara, jam’yya ta dauki wadannan matakai biyu:
Abin da ka aikata ya sabawa sashe na 21.1(viii) da (x) na tsarin mulkin jam’iyyar APC da aka yi wa karambawul."
- Shugaban APC na Jigawa
Karshen takardar ta ce akwai bukatar a cigaba da yin bincike a game da wannan zargi.
Ana lalata da mata a Borno
Mai girma Gwamnan Borno, Babagana Zulum ya gano barnar da ake yi, sai ya dauki matakin gaggawa kamar yadda ku ka samu labari.
Farfesa Zulum ya bada umarni a ruguza masa gidajen da ake lalata da ‘yan mata, da farko Gwamnati ta ba NRC filin, sai su ka bada haya.
Asali: Legit.ng