Shugaban EFCC Ya Ce Najeriya Ta Yi Asarar Naira Tiriliyan 2.9 Cikin Shekaru 3 Na Buhari
- Shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci ta EFCC, Ola Olukoyede ya bayyana gagarumar asara da kasar Najeriya ta yi tsawon shekaru uku
- Ola ya ce tsakanin shekarar 2018 zuwa 2020 na gwamnatin Muhammadu Buhari, an samu asarar Naira tiriliyan 2.9 kan badakalar kwangiloli
- Shugaban na EFCC ya bayyana haka ne yayin da ake tantance shi a majalisar Dattawa a jiya Laraba 18 ga watan Oktoba a dakin majalisar
FCT, Abuja – Sabon shugaban Hukumar EFCC, Ola Olukoyede ya ce kasar ta yi asarar Naira tiriliyan 2.9 cikin shekaru uku na badakalar kwangiloli.
Ola ya ce wannan asarar ta faru ne tsakanin shekarar 2018 zuwa 2020 wanda gwamnatin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ke mulki, Legit ta tattaro.
Asarar nawa EFCC ta ce Najeriya ta yi a mulkin Buhari?
Premium Times ta tattaro cewa Ola ya bayyana haka ne yayin da ake tantance shi a majalisar Dattawa a jiya Laraba 18 ga watan Oktoba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majalisar ta tabbatar da Olukoyede bayan shan tambayoyi daga mambobin majalisar yadda zai yaki cin hanci da rashawa.
Ola ya ce:
“Na yi bincike, inda na gano tsakanin 2018 zuwa 2020 an yi badakala a wasu hukumomi, na dauki guda daya inda na gano Najeriya ta yi asarar Naira tiriliyan 2.9 cikin shekaru uku.”
Wannan shekaru da Ola ke magana akai, tsohon shugaban kasa, Buhari ne ke jagorancin kasar wanda ya yi ikirarin yakar cin hanci da rashawa har kwano.
Wane alkawari EFCC ta yi na yaki da cin hanci?
Shugaban na EFCC ya yi alkawarin yakar cin hanci da karfinsa inda ya ce ba za su saurara wa duk wanda ya yi badakala ba komai girmansa a cikin al’umma.
Daga bisani bayan kammala tantance shi Ola ya yi godiya ga majalisar inda ya yi alkawarin ba zai bai wa ‘yan kasar kunya ba a yaki da cin hanci.
Majalisar Dattawa ta aminnce da nadin shugaban EFCC
A wani labarin, majalisar Dattawa ta tabbatar da nadin sabon shugaban Hukumar EFCC, Ola Olukoyede bayan kammala tantance shi a majalisar.
Majalisar har ila yau, ta amince da nadin sakataren hukumar, Mohammed Hammajoda da kuma Halima Shehu shugaban hukumar NSIPA.
Asali: Legit.ng