Kwamandan Boko Haram, Bulama Bukar, Ya Mika Wuya Ga Dakarun Sojoji a Borno

Kwamandan Boko Haram, Bulama Bukar, Ya Mika Wuya Ga Dakarun Sojoji a Borno

  • Wani kasurgumin dan ta'adda, Bulama Bukar, ya mika wuya ga dakarun rundunar sojojin Najeriya
  • Bukar ya kasance kwamanda a kungiyar ta'addanci na Boko Haram da suka addabi yankin arewa masu gabas
  • Rundunar sojin ta yi nasarar kwato makamai irin su bindigar AK 47, harsasai 7.62mm, wuka, babur da kudi N23,500

Jihar Borno - Rundunar sojojin Najeriya ta bayyana cewa wani kasurgumin kwamandan kungiyar ta'addanci na Boko Haram, mai suna Bulama Bukar, ya mika wuya ga dakarunta a yankin Gubio, jihar Borno.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da darakta labarai na rundunar soji, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu, ya saki a ranar Laraba, 18 ga watan Oktoba, a Abuja.

Dakarun sojoji
Kwamandan Boko Haram, Bulama Bukar, Ya Mika Wuya Ga Dakarun Sojoji a Borno
Asali: Getty Images

Jaridar Daily Nigerian a rahoto cewa dan ta'addan da ya mika wuya ya kasance kwamandan sansanin Boko Haram a Tapkin Chad da ke kauyen Gilima a karamar hukumar Abadam ta jihar Borno.

Kara karanta wannan

Yadda Dalibar UNILORIN Ta Sha Maganin Kwari Bayan Saurayin Da Suka Hadu a Intanet Ya Damfareta N500k

Ya kara da cewar:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Kayayyakin da aka samo daga dan ta'addan da ya mika wuya sun hada da bindigar AK 47 guda daya, makamai 5, harsasai 7.62mm guda 44, wuka daya, babur daya da kudi N23,500.
"A yanzu haka, ana daukar bayanan dan ta'addan."

A halin da ake ciki, kakakin rundunar sojin ya ce dakarun soji na nan suna aikin bude wuta domin raba kasar da tsagerun yan ta'adda, masu tayar da kayar baya da sauran miyagu a fadin kasar.

Mista Nwachukwu ya ce a kan haka ne dakarun bataliya ta 2 suka kai kautan bauna kan wasu yan ta'adda a yankin Udawa dake karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna a ranar 17 ga watan Oktoba sannan suka sheke yan ta'adda uku.

Ya ce wutan da aka bude masu ya sa sauran sun tsere, yayin da sojojin suka kwato wata bindiga dauke da harsashi 111 , babura biyu, babban rediyon sadarwa mai karfin gaske da kuma wayoyi guda biyu.

Kara karanta wannan

Budurwa Da Ita Kadai Iyayenta Suka Haifa Ta Mutu Kwanaki 12 Bayan Ta Yi Bikin Kammala Jami’a a Facebook

A cewarsa, wani soja ya rasa ransa a yayin arangamar, rahoton Leadership.

Ya kara da cewar a wannan ranar, dakarun Birgediya ta 1 sun kama wani da ake zargin yana kai alburusai a karamar hukumar Birnin Magaji da ke jihar Zamfara.

Ya ce binciken farko da aka yi ya nuna cewa wanda ake zargin yana hanyar kai wa wani shugaban ‘yan bindiga mai suna Gishiri harsashi ne.

A cewarsa, dakarun yan banga sun kwato wata jaka dauke da harsashin 7.62mm guda 224, wayar hannu daya da kuma kudi naira 4,000 daga hannunsa.

“A halin yanzu wanda ake zargin yana tsare ana ci gaba da bincikensa."

Kar ku bari ‘yan bindiga su karasa mu – ‘Dan majalisa ya kai kuka wajen gwamnati

A wani labarin, Yusuf Kure Baraje mai wakiltar mazabun Bosso/Paikoro a majalisar wakilan tarayya ya yi kira ga gwamnati ta ceci mutanensa.

A ranar Talata, Leadership ta rahoto Hon. Yusuf Kure Baraje ya na rokon gwamnatin tarayya ta yi masu maganin ‘yan bindiga a yankinsu.

A hirar da aka yi da shi, ‘dan majalisar wakilan ya kuma nuna rashin tsaro ya yi tasiri a Bosso da Paikoro wajen rabon abinci da aka yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng