“Ba Na Adawa Da Addinin Musulunci a Matsayin Minista”, Wike Ya Magantu

“Ba Na Adawa Da Addinin Musulunci a Matsayin Minista”, Wike Ya Magantu

  • Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya yi jawabi kan rahotannin da ke danganta shi da kyamar addinin Musulunci
  • A jawabin da ya yi a ranar Laraba, 18 ga watan Oktoba, Wike ya ce sam shi baya adawa da addinin Musulunci kuma baya kyamar Musulmi
  • Ya zargi masu adawa da shi da yi masa zagon kasa ta hanyar amfani da addini

Abuja - Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ya yi watsi da rahotannin da ke yawo cewa gwamnatinsa a Abuja na karfafa manufofin da suka sabawa addinin musulunci, jaridar The Nation ta rahoto.

Wike ya bayyana a ranar Laraba, 18 ga watan Oktoba, cewa masu ingiza ra’ayin addini suna yin hakan ne ta sigar yaudara domin samun karfi a siyasa.

Wike ya ce baya adawa da addinin Musulunci
“Ba Na Adawa Da Addinin Musulunci a Matsayin Minista”, Wike Ya Magantu Hoto: Nyesom Ezenwo Wike/Abdullah Aid
Asali: Facebook

Wike ya fayyace gaskiya kan zargin da ake masa

Kara karanta wannan

Wike Ya Dakata Ya Hakura da Maganar Karbe Filayen Masallatai da Cocin Abuja

Ministan ya bayyana hakan ne yayin da ya karbi bakuncin mambobin kwamitin gudanarwa na babban masallacin kasa na Abuja, karkashin jagorancin shugabansa, Etsu Nupe, mai martaba Alhaji Yahaya Abubakar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wike ya bayyana cewa bai da wani dalili na ingiza kalaman kiyayya kan kowani addini, sai dai ya goyi bayan duk wanda ke da manufa ta gaskiya.

Ya ba babban birnin tarayya tabbacin cewa ba zai yi kasa a gwiwa wajen goyon bayan kula da masallacin kasa ko cocin kasa ba, kasancewar an ayyana shi a matsayin abin tarihi na kasa.

Ministan ya kuma yi kira ga malaman addini da su yi wa’azi kan hadin kan kasa da zaman lafiya, rahoton Vanguard.

Ya ce:

"Babu gwamnati za ta yi kasa a gwiwa wajen goyon bayan kula da kayan kasa, imma na Kirista ko Musulmai.

Kara karanta wannan

Duniya Ta Yi Tir da Israila a Kan Kashe Fiye da Bayin Allah 500 Kwance a Asibiti

A jawabinsa, Etsu Nupe ya bukaci ministan da ya goyi bayan kula da aikin masallacin na kasa, wanda ya bayyana cewa an dakatar da shi tsawon lokaci yanzu.

Basaraken ya kuma roki ministan da ya karawa kwamitin lokaci domin ya bunkasa filayen da hukumar babban birnin tarayya ta mallaka masa.

Nyesom Wike ya bayyana dalilin yin aiki a gwamnatin Tinubu

A wani labarin, mun ji a baya cewa Nyesom Wike, ya ce ya yanke shawarar yin aiki tare da shugaban ƙasa Bola Tinubu ne saboda kwazonsa da kuma manufofinsa na siyasa.

Tsohon gwamnan na jihar Rivers ya bayyana haka ne a wani taron manema labarai da ya gudanar a Abuja a ranar Juma'a 13 ga watan Oktoba, inji rahoton TheCable.

Wike na ɗaya daga cikin fitattun jiga-jigan jam'iyyar adawa ta PDP da shugaba Tinubu na jam'iyyar APC mai mulki ya naɗa muƙamai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng