Majalisar Dattawa Ta Fara Tantance Sabon Shugaban Hukumar EFCC

Majalisar Dattawa Ta Fara Tantance Sabon Shugaban Hukumar EFCC

  • Shugaban hukumar EFCC da Sakataren da Bola Ahmed Tinubu ya naɗa sun bayyana a gaban majalisar dattawan Najeriya
  • Majalisar ta fara bin matakan tabbatar da su a muƙaman da shugaban ƙasa ya naɗa su bayan samun takarda a hukumance
  • Haka nan kuma an ga Halima Shehu a zaure majalisar, wadda za a tantance a matsayin shugabar hukumar shirye-shiryen jin daɗi NSIPA

FCT Abuja - Majalisar dattawan Najeriya ta fara zaman tantance Mista Ola Olukoyede, a matsayin sabon shugaban hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙi zagon ƙasa (EFCC).

Jaridar Punch ta tattaro cewa yanzu haka sabon shugaban EFCC da shugaba Tinubu ya naɗa na zauren majalisar kuma tuni aka fara tantance shi gabanin tabbatar da naɗinsa.

Zauren majalisar dattawa.
An fara tantance shugaban EFCC Hoto: NGRSenate
Asali: UGC

Rahotanni sun nuna cewa yanzu haka ana ci gaba da bin matakan tantance shi a zauren majalisar dattawa da ke babban birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Majalisar Dattawa Ta Yi Sauye-Sauye, Ta Naɗa Sanatocin APC Biyu a Manyan Muƙamai

Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Ola Olukoyede a matsayin shugaban EFCC ne bayan dakatar da Abdulrasheed Bawa, kusan watanni huɗu kenan da suka shige.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwanan nan ne Tinubu ya ba da izinin nada Olukoyede a matsayin Shugaban Hukumar EFCC, kuma nadin zai tabbata ne da amincewar Majalisar Dattawa.

Bayan haka wasu bayanai sun nuna sabon sakataren hukumar EFCC da shugaban ƙasa ya naɗa, Muhammad Hassan Hammajoda, ya halarci majalisar kuma an fara tantance shi.

Sabuwar shugabar NSIPA ta bayyana a gaban Sanatoci domin tantance ta

A rahoton jaridar The Nation, sabuwar shugabar hukumar kula da tsare-tsaren walwala ta ƙasa (NSIPA), Misis Halima Shehu, ta bayyana a gaban Sanatoci domin tabbatar da naɗinta.

An tattaro cewa yanzu haka majalisar ta fara aikin bin matakan tabbatar da waɗan nan naɗe-naɗe da shugaban ƙasa ya yi kuma ya nemi amincewarta.

Kara karanta wannan

Mutane Sun Kama Zanga-Zanga a Majalisa Kan Nadin Shugaban EFCC da Aka Yi

Majalisar Dattawa Ta Naɗa Sabon Jagora da Mataimakin Mai Tsawatarwa

A wani rahoton na daban kuma Majalisar dattawa ta naɗa Sanata Oyelola Yisa Ashiru (APC, Kwara ta Kudu) a matsayin sabon mataimakin jagoran majalisa.

Bayan haka ta naɗa Sanata Oyelola Yisa Ashiru (APC, Ebonyo ta Arewa) a matsayin mataimakin mai tsawatarwa na majalisar dattawan Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262