Gwamna Zulum Ya Umarci a Gudanar da Bincike Kan Gawar Diyar Dan Majalisa da Aka Halaka

Gwamna Zulum Ya Umarci a Gudanar da Bincike Kan Gawar Diyar Dan Majalisa da Aka Halaka

  • Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya bayar da sabon umarni bayan miyagu sun halaka ɗiyar ɗan majalisa a Borno
  • Gwamna Zulum ya bayar da umarni ga jami'an tsaro da su gudanar da bincike gawar marigayiyar wacce aka halaka a ranar Talata, 17 ga watan Oktoba
  • Rundunar ƴan sandan jihar ta cafke mijin marigayiyar wanda shi ne ya ɗauki gawarta ya kai ofishin ƴan sanda bayan an halaka ta

Jihar Borno - A ranar Talata, 17 ga watan Oktoban 2023, wasu miyagu suka halaka Fatima Bukar, ɗiyar ɗan majalisar dokokin jihar Borno mai wakiltar mazaɓar Ngala, Hon. Bukar Abacha.

Lamarin dai ya auku ne a kusa da unguwar Dikechiri Bayan Gidan Dambe a birnin Maiduguri babban birnin jihar Borno.

Zulum ya umarci a gudanar da bincike kan kisan Fatima
Gwamna Zulum ya yi umarni a gudanar da bincike kan gawar Fatima Hoto: @GovBorno
Asali: Twitter

Mijin marigayiyar wacce aka halaka, wanda ya kai gawarta ofishin ƴan sanda, ya ce ya tarar da gawarta a gidansa ɗaure da hannunta da ƙafafunta a bayanta yayin da yaronta ɗan shekara biyu ke kuka a gefenta, rahoton TheCable ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Yan Majalisar Dokokin Jihar APC Sun Dakatar da Tsige Mataimakin Gwamna, Sun Bayar da Dalili

Sai dai, rundunar ƴan sanda ta Gwange ta garzaya da gawar marigayiyar zuwa asibitin koyarwa na jami'ar Maiduguri domin gudanar da bincike.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An cafƙe mijin marigayiya Fatima

A halin da ake ciki, rundunar ƴan sandan jihar Borno ta cafke Adam Alhaji Ibrahim, mijin mamaciyar, Fatima Alhaji Bukar, cewar rahoton Leadership.

Wata majiya a daga ɓangaren iyalan marigayiyar ta ce an kama Adam ne a daren ranar Talata, 17 ga watan Oktoban 2023.

Wane umarni gwamna Zulum ya bayar?

Kamun na Adam ya biyon bayan umarnin da gwamnan jihar, Babagana Umara Zulum, ya bayar ga hukumomi da su mayar da gawarta zuwa asibitin koyarwa na jami’ar Maiduguri domin a yi bincike kan gawar.

Ƙafin umarnin gwamnan dai, iyalanta sun shirya jana'izar ta da karfe 2:00 na rana a ranar Laraba, 18 ga watan Oktoba, a gida mai lamba 707 a birnin Maiduguri.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Miyagu Sun Je Har Cikin Gida Sun Halaka Diyar Babban Dan Majalisa

Yan Bindiga Sun Sace Hakimi

A wani labarin daban kuma, wasu miyagun ƴan bindiga sun kai mummunan hari a ƙauyen Bagega na ƙaramar hukumar Anka ta jihar Zamfara.

Ƴan bindigan a yayin harin sun halaka mutum uku tare da yin awon gaba da Hakimin ƙauyen tare da ɗiyarsa da wasu mutane masu yawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel