Miyagu Sun Halaka Diyar Dan Majalisar Dokokin Jihar Borno a Gidan Mijinta

Miyagu Sun Halaka Diyar Dan Majalisar Dokokin Jihar Borno a Gidan Mijinta

  • An shiga jimami a birnin Maiduguri na jihar Borno kan aukuwar wani lamari na rashin imani mara daɗin ji
  • Wasu miyagu ne dai suka halaka ɗiyar wani ɗan majalisar dokokin jihar Borno a gidan mijinta a cikin birnin na Maiduguri
  • Rundunar ƴan sandan jihar ta tabbatar da aukuwar lamarin, inda ta sha alwashin zaƙulo masu hannu a kisan domin su fuskanci hukunci

Jihar Borno - Wasu miyagu da ba a san ko su wanene ba, sun je gidan mijin ɗiyar ɗan majalisar dokokin jihar Borno mai wakiltar Ngala, Bukar Abacha, inda suka halaka ta har lahira.

Zagazola Makama ya rahoto cewa an halaka marigayiyar ne ta hanyar shaƙe ta har sai da ta daina numfashi, a gidan mijinta da ke kusa da gidan Dembe da ke birnin Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Jihar APC Ta Yi Magana Kan Batun Sake Fitar da Gwamna Mara Lafiya Kasar Waje Domin Jinya

An halaka diyar dan majalisa a jihar Borno
An halaka diyar dan majalisar dokokin jihar Borno Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Lamarin mara daɗin ji dai ya auku ne a ranar Talata, 17 ga watan Oktoban 2023.

Bayanai sun nuna cewa mijinta ne ya ɗauki gawarta ya kai ofishin ƴan sanda, inda ya shaida musu cewa  ya tarar da gawarta a gidansa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda lamarin ya auku

Mijin ya gaya wa ƴan sandan cewa ya tarar an ɗaure mata hannayenta ta baya da ƙafafunta, sannan yaronta mai shekara biyu a duniya yana gefe guda yana ta tsala kuka.

Rundunar ƴan sanda ta Gwange da ke birnin Maiduguri ta garzaya da gawar marigayiyar zuwa asibitin koyarwa na jami'ar Maiduguri domin gudanar da bincike.

Mutane sun shiga tashin hankali bayan aukuwar lamarin, inda suka yi ta dandazo zuwa wajen domin ba idanunsu abinci kan abin da ya faru.

Wane martani ƴan sanda suka yi?

Jaridar TheCable ta ce kakakin rundunar ƴan sandan jihar, Kamilu Sani, ya tabbatar da aukuwar lamarin a safiyar ranar Laraba, 18 ga watan Oktoban 2023.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: 'Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Hari Gidan Ɗan Majalisar Arewa, Sun Tafi da Matarsa da 'Ya'yansa

"Eh tabbas mun samu rahoton aukuwar kisan, amma ba mu tabbatar da ko ƴan bindiga ne ko kisan gilla ba har ya zuwa yanzu." A cewarsa.

Rundunar ƴan sandan jihar ta kuma lashi takobin gano waɗanda ke da hannu a mummunan kisan domin su fuskanci hukuncin da ya da ce da su.

Yan Bindiga Sun Sace Iyalin Dan Majalisa

A wani labarin kuma, wasu miyagun ƴan bindiga sun kai farmaki gidan majalisar dokokin jihar Kwara mai wakiltar mazaɓun Ipaiye/Malete/Olooru a ƙaramar hukumar Moro.

Ƴan bindigan a yayin harin da suka kai a cikin tsakar dare, sun yi awon da mata da ƴaƴan biyu na ɗan majalisar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng