Abubuwan Sani Dangane da Sabon Shugaban Hukumar ICPC

Abubuwan Sani Dangane da Sabon Shugaban Hukumar ICPC

  • Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ICPC ta samu sabon shugaba wanda zai jagoranci tafiyar da al'amuranta
  • Dakta Musa Adamu Aliyu wanda gogaggen lauya ne ya zama sabon shugaban hukumar biyo bayan naɗin da Shugaba Tinubu ya yi masa
  • Musa Adamu haifaffen jihar Jigawa ne wanda ya kuma taɓa riƙe muƙamin babban lauyan jihar Jigawa da wasu manyan muƙamai

FCT, Abuja - A ranar Talata, 17 ga watan Oktoban 2023, Shugaba Bola Tinubu, ya naɗa Dakta Musa Adamu Aliyu a matsayin shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC.

Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Cif Ajuri Ngelale ne ya sanar da naɗin a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata.

Abubuwan sani dangane da sabon shugaban ICPC
Abubuwan sani dangane da sabon shugaban hukumar ICPC da Tinubu ya nada Hoto: @iamAhmadOlolu, @officialABAT.
Asali: Twitter

Ana sa ran Aliyu zai fara aiki bayan majalisar dattawa ta amince da naɗin da aka yi masa.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Rushe Shugabannin Gudanarwa Na NAHCON, Ya Nada Sabon Shugaba

Naɗin na Dakta Adamu Aliyu na zuwa ne kwanaki kadan bayan Tinubu ya nada Ola Olukoyede a matsayin shugaban Hukumar EFCC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abubuwan sani dangane da Dakta Musa Adamu Aliyu

Ga abubuwa biyar da ya kamata ku sani game da sabon shugaban ICPC:

  • Aliyu ɗan ƙaramar hukumar Birnin Kudu ne a jihar Jigawa.
  • Ya yi digirnsa na farko, digirin digir (MSc) da digirin digir-gir (PhD) a fannin Shari’a.
  • Ya riƙe muƙamai da dama a ƙungiyar lauyoyi ta ƙasa (NBA) reshen jihar Kano. Ya riƙe muƙamin mataimakin shugaban NBA reshen Kano daga 2016-2017, shugaban kwamitin kare hakkokin ɗan Adam na NBA reshen Kano, 2016-2017, sakataren kwamitin cigaba da ilimin shari'a 2014-2016 kuma memba na kwamitin yaki da cin hanci da rashawa 2012-2014.
  • An nada shi babban lauyan jihar Jigawa a watan Satumban 2019
  • An kuma nada shi a matsayin babban lauyan Najeriya (SAN) a watan Oktoba 2023.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Shugaba Tinubu Ya Aike da Wasika Ga Majalisar Dattawa Kan Shugaban EFCC

Shugaba Tinubu Ya Nada Sabon Shugaban NAHCON

A wani labarin kuma, shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da naɗin Alhaji Jalal Ahmad Arabi a matsayin sabon shugaban hukumar Alhazai ta ƙasa (NAHCON).

Naɗin na Arabi dai na zuwa ne bayan shugaban ƙasar ya rushe shugabannin gudanarwa na hukumar ta NAHCON.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng