Hadimin Gwamnan Katsina Ya Riga Mu Gidan Gaskiya a Hadarin Mota

Hadimin Gwamnan Katsina Ya Riga Mu Gidan Gaskiya a Hadarin Mota

  • Allah ya yi wa babban mai taimaka wa gwamnan Katsina kan ilimin addinin Islama, Dr Shamsuddeen Abubakar rasuwa
  • Marigayin ya riga mu gidan gaskiya ne sakamakon haɗarin motan da ya rutsa da shi a hanyar koma wa Katsina daga Kaduna
  • Babban mai taimaka wa gwamna kan harkokin kafafen sada zumunta, Isah Miqdad ya tabbatar da haka ga wakilin Legit Hausa

Jihar Katsina - Babban mai taimaka wa gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, kan harkokin ilimin addinin Musulunci, Dakta Shamsuddeen Abubakar ya riga mu gidan gaskiya.

Marigayin ya rasu ne sakamakon haɗarin motan da ya rutsa da shi a hanyarsa ta koma wa gida Katsina daga jihar Kaduna.

Hadimin gwamnan Katsina ya rasu a hatsarin mota.
Hadimin Gwamnan Katsina Ya Riga Mu Gidan Gaskiya a Hadarin Mota Hoto: Isah Miqdad
Asali: Twitter

Babban mai taimaka wa gwamna Raɗɗa kan harkokin digital midiya, Isah Miqdad ne ya tabbatar da rasuwar Abubakar ga wakilin Legit Hausa.

Kara karanta wannan

Katsina: Bayan Kafa Rundunar Tsaro, Gwamnatin Radɗa Ta Yi Magana Kan Yiwuwar Tattaunawa da 'Yan Bindiga

Gwamnatin Katsina ta tabbatar da rasuwar

Miqdad ya wallafa sanarwan rasuwar Malam Shamsu a shafinsa na manhajar X wanda aka fi sani da Twitter a kwanakin baya da yammacin ranar Talata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa Dakta Abubakar ya rasu ne da sanyin safiyar yau Talata, 17 ga watan Oktoba, 2023, kana ya masa fatan samun rahamar Allah.

Sanarwan ta ce:

"Da zuciya mai nauyi ina mai sanar muku da rasuwar babban mai taimaka wa gwamna Katsina kan harkokin ilimin addinin Islama, Dakta Shamsuddeen Abubakar."
"Ya rasu ne da sanyin safiyar yau (Talata), muna Addu'ar Allah ya jiƙansa ya gafarta masa, Ameen."

Yayin da muka tuntuɓi hadimin gwamna, Isah Miqdad ta wayar salula ya tabbatar mana da rasuwar Malam Abubakar da safiyar Talata.

Ya shaida mana cewa ya rasu ne sakamakon haɗarin mota a hanyarsa ta dawo wa jihar Katsina daga Kaduna.

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi Ya Soki Amurka a Kan Goyon Bayan Israila Wajen Hallaka ‘Yan Gaza

Haka nan kuma wani ganau da abun ya faru a idonsa ya shaida Legit Hausa cewa hatsarin ya auku ne a kusa da makarantar sojoji NDC da ke jihar Kaduna.

"Duk mai rai mamaci ne amma a gabana aka yi wannna hatsarin ɗazu da safe a kusa da NDC, Allah ya gafarta masa," in ji shi.

'Yan Bindiga Sun Fasa Gidan Dan Majalisa, Sun Sace Matarsa da 'Yayansa

A wani rahoton kuma Yan bindiga sun yi garkuwa da mata ɗaya da 'ya'ya biyu na wani ɗan majalisar dokokin jihar Kwara da tsakar dare.

Rahoto ya nuna cewa maharan sun kutsa cikin gida, suka tafi da su da misalin ƙarfe 1:00 na dare kuma har yanzu ba a gansu ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262