Majalisar Dattawa Ta Shiga Zaman Sirri Bayann Ndume Ya Soki Sanata Akpabio

Majalisar Dattawa Ta Shiga Zaman Sirri Bayann Ndume Ya Soki Sanata Akpabio

  • Majalisar dattawa ta ayyana shiga zaman sirri bayan Sanata Ali Ndume ya kalubalanci shugaban majalisar, Godswill Akpabio
  • Sanatan ya fara da korafin cewa yanayin yadda ake tafiyar da harkokin majalisar ya saɓa doka amma Akpabio ya hana shi ƙarisa wa
  • Nan take ya fice daga zauren majalisar kafin daga bisani aka kira shi ya dawo, suka shiga zaman sirri

FCT Abuja - Majalisar dattawan Najeriya a ranar Talata ta shiga zaman gaggawa na sirri bayan Mai tsawatarwa, Sanata Ali Ndume, ya yi ƙorafin cewa ana karya doka.

Ndume ya koka kan yadda ake yi wa doka hawan kawara a wurin tafiyar da harkokin majalisar dattawa ta 10, kamar yadda Daily Trust ta ruwaoto.

Shugaban majalisar dattawa da Sanata Ndume.
An shiga zaman sirri a majalisar dattawa Hoto: Godswill Akpabio, Ali Ndume
Asali: Facebook

Sanata Ndume ya tabo batun ne da nufin jawo hankalin shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, kan yadda yake tafiyar da harkokin majalisar wanda ya sabawa ka’ida

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi Ya Soki Amurka a Kan Goyon Bayan Israila Wajen Hallaka ‘Yan Gaza

Ndume, wanda ya fito daga jihar Borno, ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Mai girma shugaban majalisa akwai wasu abubuwa da muke yi a wannan zauren da suka saba wa ka’ida. Yallabai, babu wanda ya girmi ya koyi..."

Sanata Akpabio bai bari Ndume ya kai ga kammala jawabinsa ba ya katse shi, ya janye damar maganar da ya ba shi, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Ndume ya fice daga zauren majalisa

Ndume, wanda ya nuna ƙarara a fuskarsa cewa ya ji haushin abin da aka masa, ya sa ƙafa ya fice daga zauren majalisar inda ya nufi ofishinsa kai tsaye.

Yana zaune sai ga wani abokin aikinsa ya kira shi ya faɗa masa cewa ya koma zauren majalisa domin gudanar da zaman zartarwa na sirri.

Har zuwa yanzu da muka haɗa wannan rahoton, majalisar na kan gudanar da taron ba su kammala ba.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Ɗumi: Rigima Ta Ɓalle a APC, Shugaban Majalisar Dattawa Ya Maida Martani Kan Zargin da Aka Masa

Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan wasu Sanatoci ciki har da Ali Ndume sun kalubalanci Akpabio bisa zartar da wasu kudirori ba tare da Sanatoci sun sani ba.

Shugaba Tinubu Ya Kaddamar da Tallafin Kudi Ga Gidaje Miliyan 15

A wani rahoton Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ƙaddamar da shirin rabon tallafin kuɗi ga gidaje miliyan 15 domin rage musu raɗaɗi.

Sabon shirin rabon tallafin kuɗaɗen dai zai amfani ƴan Najeriya miliyan 62 waɗanda ke fama da matsanancin talauci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262