Dalla Dallar Yadda Najeriya Ta Ke Shirin Kashe Naira Tiriliyan 26 a Shekarar 2024

Dalla Dallar Yadda Najeriya Ta Ke Shirin Kashe Naira Tiriliyan 26 a Shekarar 2024

  • Gwamnatin tarayya ta na shirye-shiryen ganin an kammala aikin kasafin kudi nan da Disamba, za a iya kashe Naira Tiriliyan 26
  • Ministan kasafi da tsare-tsaren kasa, Atiku Abubakar Bagudu ya nuna fiye da 30% na kudin nan za su tafi ne a wajen biyan bashi
  • Sanata Atiku Bagudu ya ce sun yi hasashen farashin gangar mai a kan $73.96 sai aka bar darajar $1 a N700 a kasafin kudin 2024

Abuja - A karshen zaman majalisar FEC na makon nan, an fahimci gwamnatin tarayya ta fara shirye-shirye a kan kasafin kudin 2024.

Kamar yadda rahoto ya fito daga This Day, ana harin batar da N26.01tr a shekarar badi.

A lissafin da gwamnatin kasar ta yi, an bar farashin gangar mai a kan $73.96 da niyyar za a rika tace ganguna miliyan 1.7 a kowace rana.

Kara karanta wannan

Yadda Tinubu Ya Yi Bindiga da Naira Miliyan 400 a Kan Otel a Taron UN a Amurka

Taron FEC
Bola Tinubu a taron FEC Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

An tsaida kudin canji da farashin ganga

Yayin da ‘yan fansho za su ci Naira tiriliyan 7.78, gwamnati ta tsaida farashin Dala $1 kan N700.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga cikin wannan Naira tiriliyan 26 da ake tunanin kashewa a shekara mai zuwa, Naira tiriliyan 8 za su tafi ne ga biyan tsofaffin bashi.

Gwamnatin za ta warewa biyan albashi da sauran kashe-kashe Naira tiriliyan 10.26, sai Naira tiriliyan 1.3 ga masu cin gashin kan su.

Majalisar FEC mai ikon zartarwa a Najeriya ta kuma amince da tsarin MTEF/FSP na duk kudin da gwamnati za ta kashe daga 2024-2026.

The Cable ta tabbatar da cewa yanzu Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu za ta gabatar da MTEF/FSP gaban majalisa domin amincewarsu.

Ministan kasafi da tsare-tsaren kasa, Atiku Abubakar Bagudu ya shaida haka da ya ke zantawa da ‘yan jarida bayan taron a Aso Rock.

Kara karanta wannan

Gaza: Saudiyya Ta Kira Taron Musulmai, Fafaroma Ya Tsawata Wa Isra'ila

Atiku Abubakar Bagudu ya kuma nuna ba da dadewa ba za su gabatar da kwarya-kwaryar kasafin kudi saboda karin albashin ma’aikata.

Ministan ya sha alwashi za a rika gabatar da kundin kasafi a karshen Disamba ta yadda za a cigaba da lissafi daga Junairu zuwa Disamba.

Gwamnatin Tinubu za ta ci bashi

Ku na da labari Mai girma Bola Tinubu ya na so ya karbo $400m da za a raba a gidajen talakawa miliyan 15, kowane zai samu N25, 000.

Duk da alwashin daina karbo bashi, gwamnatin tarayya ta na bin bankin duniya domin ta ci bashi, an fahimci an amince da wasu bashin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng