Gwamnatin Bola Tinubu Ta Canza Ranar Taron FEC Daga Laraba Zuwa Litinin
- Gwamnatin tarayya karkashin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya canza ranar gudanar da taron majalisar zartarwa FEC
- Ministan yaɗa labarai, Mohammed Idris, ya ce FG ta amince da maida taron ranar Litinin daga ranar Laraba kuma ba a ko da yaushe ba
- Tun bayan rantsar da majalisar ministocinsa a watan Agusta, sau biyu kacal shugaba Tinubu ya jagoranci taron FEC
FCT Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya sauya ranar da za a riƙa yin taron mako-mako na majalisar zartarwa ta tarayya (FEC).
Channels tv ta tattaro cewa shugaban ya canza ranar taron FEC daga ranar Laraba zuwa ranakun Litinin na kowane mako.
Ministan yaɗa labarai, Mohammed Idris, shi ne ya bayyana haka yayin da yake jawabi da masu ɗauko rahoton gidan gwamnati a birnin tarayya Abuja ranar Litinin.
Da yake jawabi jim kaɗan bayan kammala taron FEC na wannan makon a fadar shugaban ƙasa, Ministan ya ce daga yanzu za a riƙa taron majalisar ranar kowace Litinin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban ƙasa, Bola Tinubu dai ya gudanar da tarukan FEC sau biyu kacal tun bayan rantsar da majalisar ministocinsa a watan Agustan da ya gabata, Daily Trust ta ruwaito.
Taron FEC karo na biyu karkashin shugaba Tinubu wanda aka gudanar a ranar litinin ya kuma shaida rantsar da karin ministoci uku da majalisar dokokin kasar ta tantance a kwanakin baya.
Ba kowane mako za a riƙa yin taron FEC ba - Idris
Ministan yada labarai ya ƙara da bayanin cewa mai yiwuwa taron na FEC ba za a riƙa yinsa a kai a kai ba musamman idan babu wani abu mai matukar muhimmanci da za a tattauna.
Wannan dai na zuwa ne yayin da ake ta cece-kuce kan rashin gudanar da taron FEC a kai a kai kamar yadda aka saba a gwamnatin da ta gabata.
Karkashin gwamnatin magabacinsa, shugaban kasa Muhammadu Buhari, an saba gudanar da tarukan FEC a kowace ranar Laraba.
Zan Iya Sadaukar da Rayuwata Domin Kawo Karshen Yan Bindiga a Katsina, Radda
A wani rahoton kuma Malam Dikko Umaru Radda ya ce a shirye yake ya sadaukar da rayuwarsa domin Ƙatsina ta samu zaman lafiya.
Gwamnan ya ce tsaro shi ne abin da gwamnatinsa ta fi ba fifiko bisa haka ya yi dokar kafa rundunar tsaron da ya kaddamar.
Asali: Legit.ng