Ma’aikata Sun Rufe Ofis Saboda ba Su Kaunar Shugabar da Tinubu Ya Nada Masu
- Rikici yanzu aka fara a Hukumar NIPOST a sakamakon sanar da nadin sababbin shugabanni da shugaban kasa ya yi
- Daga baya fadar shugaban kasa ta lashe amai, ta soke mukamin da ta ba Tola Odeyemi, aka bar Adeyemi Adepoju a kujerarsa
- Masu kaunar shugaban na NIPOST sun hana Odeyemi shiga ofis, su na ta zanga-zanga a babban ofishinsu da ke Abuja
Abuja - Wasu ma’aikatan hukumar NIPOST ta kasa, sun rufe babban ofishinsu da ke birnin tarayya Abuja a kan nadin shugaba.
Rigimar da ake yi ta na da alaka ne da nadin Tola Odeyemi a matsayin wanda za ta jagoranci hukumar kasar a cewar Daily Trust.
A sanarwar da aka fitar a makon jiya, Mai magana da yawun shugaban kasa watau Ajuri Ngelale ya ce an canza shugaban NIPOST.
Fadar shugaban kasa ta na gaba da baya
Kamar yadda mu ka kawo maku rahoto a kan lamarin, kafin a je ko ina kuma sai ga wata sanarwa da ta nuna an soke nadin da aka yi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hukumar ta NIPOST ta tabbatar da cewa Sunday Adeyemi Adepoju zai cigaba da zama a kan kujerarsa bayan amincewar Bola Tinubu.
Hakan ya na nufin an fasa nada Tola Odeyemi a matsayin shugaba yayin da sauran nadin da aka yi a ma’aikatar sadarwa su ka tabbata.
Tola Odeyemi ta shiga ofis NIPOST
A farkon makon nan sai Odeyemi ta yi yunkurin shiga ofis da sunan cewa an ba ta mukami, rahoton ya ce hakan ya jawo hayaniya.
Ma’aikatan da su ka barke da zanga-zanga sun hana sabuwar shugabar ta su shiga hukumar, har ta kai ga iya zama a kan kujerarta.
Wadannan ma’aikata da ke dauke da takardu sun nuna su na goyon bayan Adeyemi Adepoju wanda yake jagorantarsu tun a bara.
A wake-waken da su ke yi, sun tabbatar da ba su kaunar Odeyemi ta shugabance su.
Daga baya sai labari ya zo daga Daily Trust cewa sabuwar shugabar ta samu damar shiga ofis, kuma ta yi zama da manyan Darektoci.
Misis Odeyemi ta zauna a kujera dabam da wanda aka mika mata. A tarihi, ba a taba samun mace da ta rike shugabancin NIPOST ba.
Muhammadu Buhari ya nada Sunday Adepoju a 2022, sai Bola Tinubu ya bada sanawar tsige shi tare da na NCC da NIGCOMSAT.
NIPOST: Tola Odeyemi v Adeyemi Adepoju
A rahoton da mu ka fitar, mun yi tunanin Tola Odeyemi da aka sanar a matsayin sabuwar shugabar NIPOST ta hakura da kujerar.
Shugaban NIPOST mai-ci, Sunday Adeyemi Adepoju ya nuna ba zai bar mukamin da ya ke kai ba, kuma a karshe sanarwa ta zo da haka.
Asali: Legit.ng