Akwai Yiwuwar Sabon Gwamna Ya Yi Fatali da Tsare-Tsaren Emefiele da Buhari a CBN

Akwai Yiwuwar Sabon Gwamna Ya Yi Fatali da Tsare-Tsaren Emefiele da Buhari a CBN

  • Da alama Olayemi Micheal Cardoso ya raba jiha da wanda ya gabace shi a kujerar gwamnan bankin CBN watau Mista Godwin Emefiele
  • Sabon gwamnan da majalisar dattawa ta tantance zai zo da na shi tsare-tsaren na dabam domin kokarin habaka tattalin arzikin Najeriya
  • Shirin canjin manyan takardun kudi, eNaira da noman shinkafa ba za su samu wuri karkashin jagorancin Olayemi Micheal Cardoso ba

Abuja - A matsayinsa na gwamnan babban bankin CBN, Olayemi Micheal Cardoso, zai iya yin waje da wasu tsare-tsaren da ya gada a ofis.

Leadership ta ce babu mamaki Dr. Olayemi Micheal Cardoso ya raba bankin CBN da wasu shiri da ake ganin sun taimaki tattalin arzikin kasa.

Ana tunanin tsare-tsaren nan sun bada gudumuwa wajen fita daga matsin lambar tattalin arziki har sau biyu tsakanin shekarar 2016 da 2020.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Nemi Cin Sabon Bashin Dala Miliyan 400 Daga Bankin Duniya

Yemi Cardoso
Gwamnan CBN da Shugaban kasa Hoto: @OfficialABAT/@DrYemiCardoso
Asali: Twitter

A wajen tantance shi da majalisar dattawa ta yi, Yemi Cardoso ya tabbatar da zai soke wasu cikin abubuwan da Godwin Emefiele ya kawo a CBN.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dr. Yemi Cardoso da mataimakansa ne su ka gaji Godwin Emefiele wanda ya rike babban bankin har na shekaru tara daga 2014 zuwa 2023.

Sabon gwamnan ya nuna babu ruwansa da N63bn da ake kashewa wajen inganta ilmi da tsarin ABP da aka kawo domin noman shinkafa.

eNaira da canjin N200, N500, N1000

A lokacin da Emefiele ya ke ofis ne aka fito da eNaira, wani tsari da Cordoso zai soke.

Haka zalika jaridar ta ce sabon gwamnan babban bankin zai jinginar da maganar canjin kudi da aka kirkiro a 2022 da aka ga zabe ya karaso.

Badakar noman shinkafa a CBN

Sabon gwamnan na babban banki ya na ganin cuwa-cuwa ta cika tsarin ABP, inda wasu su ka fake da sunan noma domin wawuran kudin kasa.

Kara karanta wannan

Shinkafa Da Jerin Duka Kaya 43 Da CBN Ya Halatta Karbar Dala a Shigo Da Su

Ana ganin Cardoso bai yi na’am da shirye-shiryen da CBN ya rika kawowa domin kula da darajar Naira ba, a ra’ayinsa jama’a ba su ji dadinsu ba.

A karkashin jagorancin masanin tattalin arzikin, CBN zai ji da aikin gabansa ne kurum domin inganta darajar kudi da gyara tattalin Najeriya.

Tinubu ya jawo rudani a NIPOST

Ku na da labari Muhammadu Buhari ya nada Sunday Adepoju a 2022, sai Bola Tinubu ya bada sanawar ya tsige shi a cikin makon da ya gabata.

Shugaban na NIPOST ya nuna ba zai bar mukamin da ya ke kai ba, kuma a karshe haka aka yi, dole sai dai Tola Odeyemi ta hakura da kujerar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng