Mota Bas Ta Sheke Mutane Uku Yayin da Ta Bi Ta Kansu a Wani Yankin Jihar Legas

Mota Bas Ta Sheke Mutane Uku Yayin da Ta Bi Ta Kansu a Wani Yankin Jihar Legas

  • An ruwaito yadda wata mita ta hallaka mutane a wani yankin jihar Legas da ke Kudu maso Yammacin Najeriya
  • An bayyana samun raunukan mutane da yawa, inda hukumar LASEMA ta tabbatar da aukuwar lamarin
  • Hadarin mota da mutuwar fasinja ya zama ruwan dare a Najeriya, hakan na da nasaba da cunkoson ababen hawa

Jihar Legas - Akalla mutane uku ne suka rasa rayukansu, ciki har da tsohuwa mai shekaru 72 a yayin da wata mota ta banke mutane a a ranar Asabar da dare a jihar Legas.

A rahoton da muke samu, an ruwaito cewa, lamarin ya faru ne a kusa da tashar bas ta Gbagada da ke birnin Legas a Kudu maso Yammacin Najeriya.

Hakazalika, an baayyana cewa, tuni jami'ai suka tattara sauran wadanda suka samu raunuka akalla mutum bakwai zuwa asibitin kwararru na Gbagada, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ana Cikin Yanayi Bayan ’Yan Bindiga Sun Farmaki Motar Bas a Jihar Arewa, Mutum 1 Ya Mutu, An Raunata 2

Hadari a Legas
Yadda hadarin mota ya kashe jama'a a Legas | Hoto: Benson Ibeabuchi/Bloomberg
Asali: Getty Images

Yadda lamarin ya faru

A cewar rahoton, lamarin ya rutsa ne da wata motar fasinja mai daukar mutum 18 da kuma wata motar daukar kaya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Motar kirar Mazda mai dauke da mutane 18 a cikinta ta taso ne daga yankin Oshodi na jihar Aja, inji shaidun gani da ido.

Dr. Olufemi Damilola Oke-Osanyintolu, babbar sakataren hukumar LASEMA a jihar ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a ranar Lahadi da sanyin safiya.

Yadda hukumomi suka samu labari

Oke ya bayyana cewa, mummunan lamarin ya faru ne da misalin karfe 8 na daren ranar Asabar din da ta gabata.

A cewarsa, hukumar ta LASEMA ta samu labarin aukuwarsa ne da misalin karfe 10 ta hanyar kirarn waya da aka yi ta lambar ujila ta 112/767.

Jihar Legas na daga jihohin da ake yawan samun hadarin mota musamman duba da yawan zirganiyar jama'a da cunkoson ababen hawa.

Kara karanta wannan

Malamin Makaranta Ya Ɗebo Ruwan Dafa Kansa Bayan Ya Zane Ɗaliba Mace a Abuja

Wani hadarin da ya auku a Bauchi

A wani labarin, akalla mutane takwas ne suka mutu wasu suka jikkata a wani mummunan hatsarin mota da ta afku a hanyar Darazo dake jihar Bauchi.

Hukumar Kula da Kiyaye Hadura ta kasa FRSC ce ta tabbatar da wannan labari ta bakin Kwamandan hukumar, Yusuf Abdullahi.

A jawabinsa, ya ce hatsarin ya rutsa da wata mota kirar Sharon mai lamba BCH 456 XA ta kungiyar direbobi da ake amfani da ita don zirga-zirgan fasinjoji.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.