Barayi Sun Yi Awon Gaba da Rawanin Basarake a Jihar Ogun

Barayi Sun Yi Awon Gaba da Rawanin Basarake a Jihar Ogun

  • Rundunar ƴan sandan jihar Ogun ta tabbatar da nasarar cafke wasu ɓarayi da ake zargi da laifin sace rawanin wani basarake
  • Ɓarayin dai sun kutsa cikin fadar basaraken ne wanda ya riga mu cikin gaskiya, sannan suka yi awon gaba da rawaninsa tare da sandar sarautarsa
  • Kakakin ƴan sandan jihar ta tabbatar da cewa an ƙwato rawanin basaraken amma ba a kai ga ƙwato sandar sarautar ba

Jihar Ogun - Wasu da ake zargin ɓarayi ne sun shiga fadar Olu na garin Ogunmakin da ke ƙaramar hukumar Obafemi-Owode a jihar Ogun, Oba James Sodiya, inda suka yi awon gaba da rawaninsa da sandar sarautarsa.

Ƴan barandan sun shiga fadar marigayin Sarkin ne wanda ya rasu kimanin watanni biyu da suka gabata a ranar Alhamis 12 ga watan Oktoban 2023.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Dakarun Sojoji Sun Ceto Daliban Jami'ar FUGUS, Bayanai Sun Bayyana

Barayi sun sace rawanin basarake a Ogun
Barayi sun sace rawanin babban basarake a Ogun Hoto: Nigerian Police Force
Asali: Facebook

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Ogun, Omolola Odutola, ta tabbatar wa manema labarai aukuwar lamarin a birnin Abeokuta, ranar Asabar, 14 ga watan Oktoban 2023, cewar rahoton Daliy Trust.

Ko an cafke waɗanda ake zargin?

Sai dai, Odutola ta bayyana cewa ƴan sanda sun cafke mutum uku da ake zargi da aikata laifin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Odutola, wacce ta bayyana lamarin a matsayin abin ƙyama, ta ce ƴan sanda sun kwato rawanin amma har yanzu ba su ƙwato sandar ba, rahoton Daily Post ya tabbatar.

A kalamanta:

"Waɗanda ake zargin, Oke Oladipupo, Amusa Kazeem da Johnson Oluwo sun shiga gidan da aka ajiye kayayyakin basaraken da misalin ƙarfe 2:00 na ranar 12 ga watan Oktoban 2023.
“Ba a ƙwato sandar basaraken ba, amma ana cigaba da ɗaukar tsauraran matakai domin kwato su. An kama waɗanda ake zargin kuma ana kan yi musu tambayoyi.”

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Yan Bindiga Sun Sake Sace Dalibai a Jami'ar Gwamnatin Tarayya Da Ke Gusau, Bayanai Sun Fito

Ta ce kwamishinan ƴan sandan jihar , Abiodun Alamutu, ya yi kira ga jama’a da su bayar da bayanan da za su kai ga kwato sandar ofishin.

Ba a Biya Ko Sisi Ba Kafin Saki Daliban Jami'ar NSUK, Gwamna

A wani labarin kuma, gwamnan jihar Nasarawa ya bayyana cewa ko sisi ba a biya ba kafin a sako ɗaliban jami'ar jihar da ƴan bindiga suka sace.

Gwamna Abdullahi Sule ya bayyana cewa ƙoƙarin da jami'an tsaro suka yi ne ya yi sanadiyyar ceto ɗaliban cikin ƙoshin lafiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng