"Na Gode Wa Allah An Kama Mu", Mai Garkuwa Bayan Yan Sanda Sun Kama Shi
- Auwal Abdullahi, wani hatsabibin mai garkuwa da mutane ya ce ya gode wa Allah da jami'an yan sanda suka kama shi
- Kakakin yan sandan Najeriya, Muyiwa Adejobi, ya ce an kama Abdullahi ne a ranar 12 ga watan Satumban 2023 a karamar hukumar Soba, Kaduna
- Abdullahi, wanda ya amsa cewa shi mai garkuwa ne, ya ce yana cikin wadanda suka sace dalibai a Kwalejin Gwamnatin Tarayya, Yauri, Jihar Kebbi
Jihar Kaduna - Rundunar Yan Sandan Najeriya, NPF, ta ce ta kama wani Auwal Abdullahi, wani hatsabibin mai garkuwa da mutane a jihar Kaduna.
Yayin gabatar da su ga manema labarai a ranar Juma'a, Muyiwa Adejobi, Kakakin yan sanda, ya ce an kama Abdullahi ne a ranar 12 ga watan Satumban 2023, a Kauyen Garu, Karamar Hukumar Soba, rahoton The Cable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tare da ni aka sace daliban FGC Yauri - Wanda ake zargi da garkuwa
Abdullahi ya amsa cewa da shi aka sace wasu daliban Kwalejin Tarayya Ta Gwamnati, FGC, Yauri, Jihar Kebbi.
A ranar 17 ga watan Yunin 2021, yan bindiga sun sace dalibam FGC Birnin Yauri daga makarantarsu.
Dakarun sojojin Najeriya sun ceto wasu cikin daliban yayin da an rahoto cewa an sako sauran bayan an biya wadanda suka sace su kudin fansa.
Yan bindigan sun sako wasu daliban 27 daga bisani sannan wasu 30 kuma aka sako su bayan watanni bakwai a tsare.
Hudu cikin daliban sun shaki iskar yanci bayan tsare su na shekaru biyu wasu uku kuma aka sako su a Mayun 2023.
Adejobi ya ce sakamakon bincikan Abdullahi, yan sandan sun kama wani Abubakar Abdullahi, kawu kuma abokin aikin Abdullahi a Zaria.
Kakakin yan sandan ya ce Abubakar ya amsa cewa ya yi aiki tare da Abdullahi wurin garkuwa da mutane sau da yawa.
Abdullahi ya ce:
"Shi (Abubakar) ya taho wuri na kuma ya bani kudi domin in tafi daji in tarar da sauran tawagar. Na godewa Allah cewa an kama mu kuma an kawo mu nan.
"Na samu N40,000 a baya daga garkuwa da mutane. Shugabanninmu ke karbar fansar."
Adejobi ya ce NPF ba za ta yi kasa a gwiwa ba a kokarinta na farautar shugabannin tawagar masu garkuwar wanda a yanzu ake nemansu.
Masu Garkuwa Sun Sace Mutane Biyu a Zaria
A wani rahoton, yan bindiga da ake zaton masu garkuwa ne, sun kai farmaki a Wusasa da ke ƙaramar hukumar Zariya ta jihar Kaduna.
Masu garkuwan a yayin harin da suka kai, sun sace wani ma'aikacin wani asibiti mai suna St. Luke, mai suna Yusha'u tare da kaninsa mai suna Joshua Peter.
Asali: Legit.ng