"Duk Dan Sanda Da Ya Yi Wa Yan Najeriya Kwacen Kudi Dan Fashi Ne", Inji Kakakin Yan Sanda

"Duk Dan Sanda Da Ya Yi Wa Yan Najeriya Kwacen Kudi Dan Fashi Ne", Inji Kakakin Yan Sanda

  • Rundunar yan sanda ta yi Allah wadai da jami'anta da ke tatsar kudi daga hannun yan Najeriya
  • Mai magana da yawun rundunar yan sanda, Olumuyiwa Adejobi, ya ce duk jami'in da ya kwace kudi daga hannun wani babu banbancinsa da dan fashi
  • Wannan ya biyo bayan kokawar da wani dan kasuwa ya yi, inda ya ce jami'an tsaro sun far ma gidansa sannan a karshe suka tatse su bayan sun kai su ofishinsu

Kakakin rundunar yan sandan Najeriya, Olumuyiwa Adejobi, ya bayyana cewa duk jami'in dan sandan da ya nunawa yan Najeriya bindiga domin ya karbi kudi daga hannunsu bai da banbanci da yan fashi, Daily Trust ta rahoto.

Wani dan kasuwar 'crypto' kuma mai fada aji a dandalin X, ya caccaki yan sanda bayan ya zargi jami'an rundunar da kutsa kai cikin gidansa tare da kama shi ta karfi da yaji.

Kara karanta wannan

Bidiyon Yan Mata Fiye Da 10 a Kan Babura Ya Girgiza Intanet, Sun Jeru Sanye Da Anko

Kakakin yan sandan Najeriya yana jawabi
"Duk Dan Sanda Da Ya Yi Wa Yan Najeriya Kwacen Kudi Dan Fashi Ne", Inji Kakakin Yan Sanda Hoto: Adejobi Olumuyiwa
Asali: Facebook

Yadda yan sanda suka tatse ni, wani dan kasuwa

Mutumin ya yi ikirarin cewa yan sandan sun shiga gidansa ne sanye da kayan gida ba tare da takardar izinin bincike ba, inda suka kwashi dukkanin mazan da ke gidan zuwa ofishinsu, suna masu yi masu tambayoyi da ikirarin cewa su masu damfara ta yanar gizo ne.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya gabatar da sakon cire kudi inda suka karbe wasu kudade daga hannusa, yayin da ya bayyana cewa sun karbi jimlar dubu dari biyar daga hannun dukkanin mutane da ke zaune a gidansa.

Wani bangare na wallafarsa na cewa:

"Wato jami'an yan sanda sun zo gidana a yammacin jiya da misalin karfe 7:00 na yamma sannan suka kwashe gaba daya mazan da ke rukunin gidajen. Duk mun kwana ne a kurkuku babu gaira babu dalili. Da aka kira mu don amsa tambayoyi wanda ya fi kama da tursasawa. Sun ce 'Kuna yin Yahoo' na karyata saboda ban ma san yadda ake yin Yahoo ba.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Sace Malamin Musulunci Yayin Da Su Ke Raka Gawa Makabarta, Bayanai Sun Fito

"Abu na gaba shine rubuta bayanai cewa imma dai ni dan kungiyar asiri ne ko dan fashi. Duk muka ki rubutawa ba tare da lauyoyinmu a wajen ba, don haka suka tilasta mana kwana a kurkuku. Da safen nan, an kwace fiye da 500k daga wajenmu gaba daya."

Da yake martani, wani mai amfani da dandalin ya ambaci sunan kakakin rundunar cewa, "A matsayinka na kakakin rundunar yan sandan Najeriya ka yi wani abu a kan wannan mummunan abu da abokan aikinka ke yi a kodayaushe. Lallai dan sanda abokinka ne"

Da yake martani, Adejobi ya ce:

"Ina ganin akwai bukatar karin haske a nan. Ya dage kan son ganin lauya, kuma ya kwana a kurkuku. Shin lauyan ya zo? An biya kudin ne a gaban lauyansa? Idan lauyan bai zo ba, me yasa baka kira wani ba. Ko an kwace wayarka daga hannunka ne? Ya kamata ya fayyace wasu abubuwa a nan. Imma ace dan sanda abokinka ne ko makiyinka ne, wani rawar gani lauyanka ya taka."

Kara karanta wannan

Tashin Hankali Yayin Da Yan Gidan Magajiya Suka Bazama Neman Kwastamomi a Kasuwar Legas

A martaninsa, wani mai amfani da dandalin X ya wallafa hoton wani martani da kakakin yan sandan ya taba yi, inda ya yi Allah wadai da kwace kudi da yan sanda ke yi.

Duk dan sandan da ya kwace kudi daga hannun yan Najeriya dan fashi ne, Adejobi

Da yake martani, Adejobi ya yi karin haske kan lamarin. Daily Trust ta nakalto yana cewa:

"Eh, har yanzu yana nan a kan haka. Duk jami'in dansa da ke rike da makami ko wani jami'in tsaro wanda ya kwace kudi ta karfi daga hannun bayn Allah yan Najeriya tamkar dan fashi ne. Karbe kudi baya daga cikin manufar hukumomin, imma dauke da makami ko a'a. Muna Allah wadai da haka, kuma hatta sufeto janar na yan sanda ya fayyace hakan.
"IGP ma ya gargadi jami'i da kada su ajiye sunansa don karbar kudi ko damfarar yan Najeriya kuma kada su karbi kowani kyauta zuwa gare shi. Mun yi sanarwa a hukumance kan haka. Ya kamata ku karanta sannan ku fahimta kafin ku yanke hukunci ko yin Allah wadai a nan."

Kara karanta wannan

Abun Bakin Ciki Yayin da Fusatattun Matasa Suka Halaka Wani Dan Achaba kan Satar Mazakuta a Abuja

An kama lauyan bogi bayan ya yi nasara a kararraki 26

A wani labari na daban, mun ji cewa wani mutumi wanda ake zargin lauyan bogi ne ya yi nasarar lashe kararraki 26 a kotu kafin aka gano shi.

An yi zargin cewa mutumin, Brian Mwenda Njagi, yana yi wa wani lauya mai irin sunansa sojan gona ne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng