“Allah Akbar”: Yadda Mahaukaciya Ta Haihu, Hotunan Kyakkyawan Jinjirin Sun Yadu

“Allah Akbar”: Yadda Mahaukaciya Ta Haihu, Hotunan Kyakkyawan Jinjirin Sun Yadu

  • Wata mata mai lalurar tabin hankali ta haifi kyakkyawan jinjiri, namiji mai ji da koshin lafiya
  • Hotunan yaron da aka wallafa a Facebook ya nuno matar da dan nata jim kadan bayan ta haihu a wani budadden wuri
  • Hotunan matar da dan nata ya tsuma zukatan masu amfani da Facebook da suka gan su, sannan sun taya ta murna

Wata mata mai lalurar tabin hankali ta haifi kyakkyawan jinjiri, kuma hotunan sun yadu.

Gabby Queens ce ta wallafa hotunan matar da danta a Facebook, kuma sun tsuma zukatan mutane da dama.

Mahaukaciya ta haifi kyakkyawan jinjiri
“Allah Akbar”: Yadda Mahaukaciya Ta Haihu, Hotunan Kyakkyawan Jinjirin Sun Yadu Hoto: Facebook/Gabby Queens
Asali: Facebook

Hotunan sun nuna cewa matar ta haihu ne a budadden wuri yayin da take zaune a bayan wani gini.

Hotunan mai lalaurar tabin hankali da ta haifi kyakkyawan jinjiri

Ta ajiye dan nata a kasa yayin da take kallonsa, Wani hoton kuma ya nuna kyakkywan fuskar dan, wanda yake fari tas.

Kara karanta wannan

Gambo Haruna: Bakanuwa Mai Marayu 6 Da Ke Sana’ar Tura Baro

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gabby bata bayyana lokaci ko a inda abun ya faru ba amma ta ce babu likitoci ko malaman jinya, amma ta haihu cikin nasara.

Ta rubuta:

"Babu likita, babu malaman jinya, babu uwa, babu taimako, babu kayan lambu, babu asibiti, amma mahaukaciyar nan ta haifi kyakkyawan jinjiri cikin ikon Allah."

Mutane da suka ga matar da dan nata sun garzaya sashin sahrhi don taya ta murna.

Masu amfani da Facebook sun yi martani ga hotunan mahaukaciyar da ta haihu

Victor Ukaigwe ta ce:

"Allah ubangiji ya albarkace ki da yaronki. Allah zai ba ki wanda zai iya kula da ke."

Onyisi Samson Hadome ya yi martani:

"Allah buwayi ne. Irin wannan kyakkyawan yaro."

Olatunde Oyebi ya ce:

"Allah shine gagara misali."

Kelsey Segun Falae ya ce:

"Allah na da girma da buwaya."

Chibless Nwaoma ta ce:

Kara karanta wannan

“Kar A Yi Gaggawan Kiran Jariri Mummuna”: Wata Uwa Ta Girgiza Intanet Bayan Ta Saki Bidiyon Sauyawar Danta

"Duk na Allah ne. Kalli yadda yaron ya yi shar da shi."

Ku daina kiran jarirai munana: Wata uwa ta baje kolin sauyawan danta

A wani labarin, wata yar TikTok @sommywhiteorganics ta girgiza intanet bayan ta saki hotunan sauyawar danta masu ban mamaki.

Uwan dan wacce ke cike da farin ciki ta saki hoton yaron yana jinjiri da kuma wani hotonsa yayin da ya fara girma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng