Gwamnatin Kano Ta Aike da Sakon Ta'aziyyar Rasuwar Sanata Bello Yusuf

Gwamnatin Kano Ta Aike da Sakon Ta'aziyyar Rasuwar Sanata Bello Yusuf

  • Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya fitar sanarwan ta'aziyya bisa rasuwar Sanata Bello Maitama Yusuf
  • Abba ya ce rashin babban mutum mai ƙima a idon jama'a kamar Sardaunan Dutse babban giɓi ne da cike shi ka iya zama ƙalubale
  • Ya jajanta wa iyalai, jihar Jigawa da Najeriya baki ɗaya, yana mai addu'ar Allah ya sa Ajannah ta zama makomarsa ta karshe

Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya yi ta'aziyyar rasuwar Sanata Bello Maitama Yusuf (Sardaunan Dutse), tsohon ministan cikin gida a Najeriya.

Gwamnan ya ayyana mutuwar Sanata Bello a matsayin babban rashi ba wai ga iyalansa kaɗai ba, har da ƙasa baki ɗaya, kamar yadda Tribune ta ruwaito.

Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Yi Ta'aziyya.
Gwamnatin Kano Ta Aike da Sakon Ta'aziyyar Rasuwar Sanata Bello Yusuf Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

A sakon ta’aziyyar da ya fitar, gwamnan ya bayyana cewa, mutuwar ta haifar da babban giɓi, wanda cike shi abu ne mai matuƙar wahala duba da irin matsayin da Sanata Yusuf ke da shi a cikin al’umma.

Kara karanta wannan

Ganduje Ya Yi Babban Kamu a Majalisa, Sanata Mai Ci Ya Sauya Sheƙa Zuwa Jam'iyyar APC

Abba ya yi wa marigayin Addu'a

Abba Gida-Gida ya kuma yi addu'ar samun rahamar Allah ga marigayi Sardaunan Dutse kana ya miƙa sakon ta'aziyya ga iyalai, jihar Jigawa da kuma Najeriya baki ɗaya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya yi addu'ar Allah ya bai wa iyalansa da ƙasa baki ɗaya haƙurin iya jure wannan babban rashi wanda cike gurbinsa ke da wahala.

Wannan na kunshe ne a wata sanarwa da sakataren watsa labaran ofishin gwamnan jihar Kano, Kwamared Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar ranar Jumu'a.

Sanarwan ta haƙaito Gwammna Yusuf na cewa:

“Marigayi Bello Maitama Yusuf babban masanin fasaha ne, malamin addinin Islama, dan siyasa, kuma hamshakin dan kasuwa, wanda ya taba rike mukamin ministan harkokin cikin gida da kasuwanci daga 1979 zuwa 1982."
"Ya kuma yi wa'adi da dama a matsayin Sanatan Tarayyar Najeriya, mai wakiltar jihar Jigawa. Allah ya jikansa da rahama, ya sa shi a cikin Aljannatul Firdausi, Ameen."

Kara karanta wannan

Majalisar Wakilai Ta Ƙasa Ta Ɗage Zamanta Yayin da Ɗan Majalisar APC Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

Za a yi jana'izar Sanata Maitama Yusuf kamar yadda addinin Musulunci ya tanada, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

An tattaro cewa za a yi Sallar jana'izar ne a Masallacin Fadar Sarkin Kano bayan Sallar Juma'a da karfe 2:30 na rana.

Mun Daina Adawa da Tikitin Musulmi da Musulmi, Shugabannin Kiristoci

Mun kawo muku rahoton cewa Kiristocin Najeriya sun canza tunani kan adawar da suka yi da tikitin Musulmi da Musulmi na Tinubu da Shettima a zaben 2023.

A wurin wani taro a Abuja, jagororin mabiya addinin Kirista sun ce.tsoron da suka ji na haɗa Musulim/Muslim ya gushe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262