Daliban Jami'ar Jihar Nasarawa Sun Shaki Iskar Yanci Daga Hannun Yan Bindiga

Daliban Jami'ar Jihar Nasarawa Sun Shaki Iskar Yanci Daga Hannun Yan Bindiga

  • Daga karshe ɗaliban jami'ar jihar Nasarawa da aka yi garkuwa da su sun shaƙi iskar 'yanci ranar Alhamis, 12 ga watan Oktoba
  • Dakarun sojin Bataliya ta 117 da ke Keffi ne suka samu nasarar ceto ɗaliban mata su huɗu bayan matsa wa yan bindigan lamba
  • Wata majiya daga jami'ar ta tabbatar da lamarin, inda ta ce sun samu labarin ɗaliban sun bar hannun masu garkuwa

Jihar Nasarawa - Ɗaliban jami’ar jihar Nasarawa hudu da aka sace sun samu ‘yanci daga hannun wadanda suka yi garkuwa da su, Leadership ta rahoto.

Idan baku manta ba, yan bindiga ɗauke da muggan makamai sun kai farmaki gidan ɗaliban da ke Angwan Ka'are a ƙaramar hukuma Keffi da sanyin safiyar Talata.

An ceto ɗaliban jami'ar jihar Nasarawa.
Daliban Jami'ar Jihar Nasarawa Sun Shaki Iskar Yanci Daga Hannun Yan Bindiga Hoto: vanguardngr
Asali: UGC

Yayin harin, 'yan ta'addan sun yi awon gaba da ɗalibai mata huɗu zuwa wani wuri da ba'a sani ba.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Gindaya Sharaɗi Kafin Su Sako Ɗalibai Mata da Suka Sace a Jami'ar Arewa

Sojoji sun kwato ɗaliban daga hannun 'yan bindiga

A halin da ake ciki, sojojin Najeriya na bataliya ta 117 da ke Keffi sun ceto daliban a ranar Alhamis bayan da suka ci gaba da matsa lamba kan masu garkuwa da su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Babban Kwamandan Bataliyar, Laftanal Kanal Auwalu Inuwa, shi ne ya bayyana haka ga wakilin jaridar Vanguard a Lafiya, babban birnin jihar Nasarawa.

Ya bayyana cewa an kubutar da daliban ne a dajin Angwan Gauta da ke karamar hukumar Keffi bayan kokarin da jami’an sojoji suka yi.

Ya ambaci sunayen daliban da aka ceto da suka hada da Rahila Hanya, Josephine Gershon, Rosemary Samuel da kuma Goodness Samuel.

Laftanar Kanar Inuwa ya kuma ba da tabbacin cewa za a miƙa daliban ga iyalan su bayan an kammala duba lafiyarsu.

Wata majiya da ta tabbatar da ceto ɗaliban ga yan jarida, ta ce:

Kara karanta wannan

Mu 100 Mu Ka Auka Makaranta, Aka Yi Awon Gaba da Yara a 2021 – ‘Dan Bindiga

“Mun samu labarin cewa daliban sun baro hannun masu garkuwa da mutane, sun shaƙi iskar 'yanci da yammacin yau (Alhamis)."

Sojoji Sun Halaka 'Yan Ta'adda 50, Sun Kama 114 Cikin Mako Daya a Arewa

A wani rahoton kun ji cewa Gwarazan dakarun sojin Najeriya sun halaka gwamman 'yan ta'adda a shiyyoyin arewa uku cikin mako ɗaya.

Hedikwatar tsaro ta ƙasa ta bayyana cewa akalla 'yan ta'adda 50 ne suka sheƙa barzahu yayin da sojojin suka ceto mutane 49.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262