Dalibin Da Ya Fi Kowa Cin JAMB a Jihar Edo Ya Zama Kakakin Majalisa Na Kwana Daya

Dalibin Da Ya Fi Kowa Cin JAMB a Jihar Edo Ya Zama Kakakin Majalisa Na Kwana Daya

  • Ɗalibin da ya fi kowa yawan maki a JAMB daga jihar Edo ya zama shugaban majalisar dokokin jihar na kwana ɗaya
  • Kakakin majalisar, Blessing Agbebaku, shi ne ya karrama shi da matsayin yayin da aka gabatar masa da ɗalibin ranar Alhamis
  • Ya kuma ba shi tallafin karatu na shekara ɗaya yayin da ɗan majalisar mazaɓarsa ya ƙara masa da tallafin shekara ta biyu

Jihar Edo - Ɗan shekara 15 din da ya fi kowa yawan samun makin jarabawar JAMB a jihar Edo, Master Gold Oviota Ajagun, ya zama shugaban majalisar dokokin jihar na kwana ɗaya.

Master Ajagun, dalibin makarantar sakandaren Gloryland da ke ƙaramar hukumar Akoko-Edo, ya zama zakara a jarrabawar share fagen shiga manyan makarantu (UTME) a jihar Edo.

Dalibin da ya zama zakara a jarabawar JAMB daga jihar Edo.
Dalibin Da Ya Fi Kowa Cin JAMB a Jihar Edo Ya Zama Kakakin Majalisa Na Kwana Daya Hoto: Kola T Sam Agidiomo
Asali: Facebook

Hukumar shirya jarabawar shiga jami'o'i (JAMB) ke shirya jarabawar UTME a kowace shekara, kamar yadda rahoton Daily Trust ya tattaro.

Kara karanta wannan

Majalisar Wakilai Ta Ƙasa Ta Ɗage Zamanta Yayin da Ɗan Majalisar APC Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

Ajagun ya samu maki 335 a jarabawar JAMB ta ƙarshe kuma hakan ya ba shi damar zama wanda ya fi kowa yawan maki a jihar Edo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ɗalibin ya ɗana kujerar shugaban majalisar dokokin Edo

Shugaban majalisar dokokin jihar Edo, Blessing Agbebaku, ya karɓi bakuncin ɗalibin, wanda ya samu rakiyar ɗan majalisa mai wakiltar Akoko-Edo II, Donald Okogbe.

Jim kaɗan bayan zuwan zaƙakurin dalibin, Agbebaku, ya naɗa shi a matsayin shugaban majalisa na kwana ɗaya tal.

Agbebaku ya yabawa dalibin bisa nasarar da ya samu da kuma sanya jihar Edo alfahari sannan kuma ya ba shi tallafin karatu na shekara guda wanda ya ƙunshi kuɗin makaranta.

A cewarsa, tallafin karatu ya fara aiki ne nan take bayan ya samu gurbin karatu a jami’ar Ibadan domin yin karatun likitanci da tiyata.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC Ya Yunƙuro, Ya Kaddamar da Sabuwar Rundunar Tsaro Domin Kawo Karshen 'Yan Bindiga

Ya samu kyautar kwanfuta za ƙarin tallafi

Tun da farko, da yake gabatar da yaron ga shugaban majalisar, Donald Okogbe ya ce ya gamsu da sakamakon da yaron ya samu kasancewar dan mazabarsa ne.

Dan majalisar, ya miƙa wa ɗalibin ƙyautar kwamfutar tafi-da-gidanka kuma ya ɗauki alƙawarin biya masa kudin karatu na shekara ta biyu.

Sanata Mai Ci Ya Sauya Sheƙa Zuwa Jam'iyyar APC

A wani rahoton kun ji cewa Sanata Ifeanyi Ubah ya sauya sheƙa daga jam'iyyar YPP ya koma jam'iyyar APC mai mulki ranar Alhamis, 12 ga watan Oktoba, 2023.

Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ne ya tabbatar da haka a wasiƙar da ya karanta yayin zamana majalisar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262