Nasarawa: Ombugadu Na PDP Ya Musanta Batun Korar Sarakunan Gargajiya Idan Ya Hau Mulki
- Wanda kotu ta ayyana a matsayin zaɓaɓɓen gwamnan jihar Nasarawa, David Ombugadu, ya musanta rahotannin da ke cewa zai kori sarakunan gargajiya
- Martanin nasa na zuwa ne bayan rahotanni sun yi yawo cewa yana shirin maye gurbin sarakunan musulmi da kiristoci
- Ombugadu ya nanata cewa a shirye yake ya yi aiki tare da dukkanin sarakunan sannan ya buƙaci kafafen yaɗa labarai da su yi taka tsantsan
Lafia, jihar Nasarawa - Ɗan takarar gwamnan jam'iyyar PDP a jihar Nasarawa, David Ombugadu, ya jaddada ƙudirinsa na yin aiki tare da dukkanin sarakunan gargajiya.
Ya tabbatar da hakan ne ta wata sanarwa da Mike Omeri, kakakin ƙungiyar yaƙin neman zaɓen jam'iyyar ya fitar a ranar Laraba, 11 ga watan Oktoba.
Bayanin hakan dai ya kasance martani ne ga jita-jita da rahotannin da ke yawo a kafafen yaɗa labarai na cewa ya yi niyyar korar duk wasu manyan sarakunan gargajiya a jihar.
Kamar yadda sanarwar wacce Legit Hausa ta samu, Omeri ya ce:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"David Ombugadu a shirye yake wajen yin aiki domin cigaban jihar Nasarawa, tabbatar da bin doka da oda, da samar da haɗin kai a tsakanin masu ruwa da tsaki, ciki har da sarakunan gargajiya."
"Bugu da ƙari, Dr. Ombugadu ba shi da wata manufa ta maye gurbin wasu sarakunan gargajiya na musulmi da kiristoci idan ya karɓi ragamar mulki."
Wane gargaɗi Ombugadu na PDP ya yi?
Sanarwar ta kuma bukaci kafafen yaɗa labarai da su tabbatar suna bin diddigin rahotannin su tare da tabbatar da cewa suna bin ƙa’idojin aikin jarida.
"Yana da matuƙar muhimmanci a kiyaye aikin jarida da kuma nisantar yaɗa labaran ƙarya da ka iya cutar da mutuncin mutane." A cewarsa.
"Dakta Ombugadu ya yi amanna da gina kyakyawar alaka da dukkanin ɓangarorin al'umma, ciki har da sarakunan gargajiya domin samar da cigaba da haɗin kai a jihar Nasarawa. Duk wani abu akasin haka ƙarya ce mara tushe."
Farfesa Mansur Ya Magantu Kan Hukuncin Zaben Nasarawa
A wani labarin kuma, sanannen malamin addinin musulunci, Sheikh Mansur Sokoto ya yi magana kan hukuncin da kotun zaɓe ta yanke a shari'ar zaɓen gwamnan jihar Nasarawa.
Malamin addinin musuluncin na ganin cewa hukuncin da kotun ta yanke, barazana ce ga musulunci.
Asali: Legit.ng