Tinubu Ya Nada Shugabanni a Hukumomin NIPOST, NCC, NITDA Da Sauransu
- Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sanar da sabbin nade-nade a ma'aikatar sadarwa da kirkire-kirkire da tattalin arzikin zamani
- Tinubu ya nada sabbin shugabanni a hukumomin NIPOST, NCC, NITDA, NIGCOMSAT da NDPC
- An kuma sanar da nadin mai ba shugaban kasa shawara ta musamman kan fasaha da tattalin arziki na zamani - Idris Aubankudi
Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da nadin shugabanni a Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC), Hukumar Aika Sakonni ta Najeriya (NIPOST), da Hukumar bunkasa ilimin fasahar sadarwa ta Najeriya (NITDA).
Sauran hukumomin da aka yi sabbin nade-nade sun hada da Hukumar kula da yanayin sararin samaniya ta kasa (NIGCOMSAT) da Hukumar kare bayanan sirrin masu amfani da intanet ta kasa (NDPC).
Mai ba shugaban kasa shawara ta musamman kan harkokin labarai, Cif Ajuri Ngelale, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya saki a ranar Laraba, 11 ga watan Oktoba.
Ngelale ya ce sabbin nade-naden da shugaban kasar ya yi suna karkashin karkashin ma'aikatar sadarwa da kirkire-kirkire da tattalin arzikin zamani.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
- Shugaban Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) - Aminu Maida
- Manajan Darakta/Shugabar Hukumar kula da yanayin sararin samaniya ta kasa (NIGCOMSAT) - Nkechi Egerton-Idehen
- Darakta Janar/Shugaban Hukumar bunkasa ilimin fasahar sadarwa ta Najeriya (NITDA) - Kashifu Inuwa Abdullahi
- Kwamishinan kasa/ Shugaban Hukumar kare bayanan sirrin masu amfani da intanet ta kasa (NDPC) - Dr. Vincent Olatunji.
- Shugaban Hukumar Aika Sakonni ta Najeriya (NIPOST) - Tola Odeyemi
Ya kuma sanar da cewar shugaban kasa Tinubu ya amince da nadin mai ba shugaban kasa shawara ta musamman kan fasaha da tattalin arziki na zamani - Idris Aubankudi.
Ya kuma bayyana cewa sabbin nade-naden sun fara aiki nan take.
Cikakken Jerin Takardun Karatun da Tinubu, Atiku, Peter Obi, Kwankwaso Suka Ba INEC Kafin Zaben 2023
Shugaba Tinubu ya bukaci majalisa ta amince da sabbin nade-nade 17
A wani labarin, shugaban ƙasa Bola Tinubu ya nemi majalisar wakilai da ta amince da naɗin shugaban da hukumar raya yankin Neja Delta (NDDC) da mambobin hukumar.
A cewar shugaba Tinubu, bukatarsa ta yi daidai da tanadin sashe na 2(2) na dokar hukumar raya yankin Neja Delta, cewar rahoton jaridar The Nation.
Ben Kalu, mataimakin kakakin majalisar wakilai, ya karanta wasikar shugaban ƙasa a zauren majalisar a ranar Talata, 10 ga watan Oktoba, rahoton Vanguard ya tabbatar.
Asali: Legit.ng