Majalisar Wakilan Tarayya Ta Dage Zama Bayan Mutuwar Ɗan Majalisa Daga Sokoto
- Majalisar wakilai ta ƙasa ta ɗage zamanta sakamakon rasuwar ɗan majalisa daga jihar Sakkwato ranar Laraba
- Mamba mai wakiltar Isa da Sabon Birni, Abdulkadir Danbuga, ya rasu yana da shekara 63 a duniya bayan fama da rashin lafiya
- Mataimakin shugaban majalisar, Ben Kalu, ya ce wannan mutuwa babban abin takaici ne ga iyalansa da ƙasar nan baki ɗaya
FCT Abuja - Majalisar wakilan tarayya ta dage zamanta da sanyin safiyar ranar Laraba domin jimamin rasuwar Abdulkadir Danbuga, dan majalisa daga jihar Sokoto.
Marigayi Danbuga, mai wakiltar mazabar Isa/Sabon Birni ta tarayya a jihar Sakkwato, ya rasu ne a ranar Laraba a Abuja yana da shekaru 63 a duniya.
Ahmad Kalambina (PDP, Sokoto) ne ya sanar da rasuwarsa a wata wasika da ya aike wa majalisar wakilan tarayya a zaman yau Laraba.
Rahoton Premium Times ya nuna cewa mataimakin kakakin majalisar, Ben Kalu, shi ne ya karanta wasiƙar ga sauran abokan aikinsa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A wani ɗan taƙaitaccen jawabi da ya yi, mataimakin kakakin majalisar ya ce mutuwa ta saba katse hanzarin ɗan Adam, ta kawo karshen burinkansa na rayuwa.
Ya ce:
“Ku dubi irin wahalar da ya sha don ya ci zabe. Kokarin da ya yi don wakiltar jama'arsa. Duk kuɗin da ya kashe da ƙoƙarin da ya yi sun gushe daga yau."
"Wannan abin bakin ciki ne, abin baƙin ciki ne ga iyalinsa abin bakin ciki ne ga al'ummar ƙasar nan. Mun zo hidimta wa kasar mu ne, abinda ya shafi ɗayanmu, ya taɓa kowa, yau ranar baƙin ciki ce ga majalisa."
Majalisa ta ɗage zamanta saboda wannan rashi
Bayan wadannan kalamai na Kalu ne sai shugaban masu rinjaye na majalisar, Julius Ihonvbere, ya miƙe ya gabatar da bukatar dage zaman har zuwa ranar Alhamis.
Dukkan 'yan majalisar suka amince da wannan buƙata wanda nan take majalisar da sanar da ɗage zaman domin jimamin rasuwar abokin aiki, Channels tv ta ruwaito.
A watan Afrilu da ya gabata, zababben dan majalisar wakilai, Isma’ila Maihanchi, daga jihar Taraba ya rasu tun kafin a rantsar da majalisa ta 10.
Kashim Shettima da Gwamnonin APC Sama da 10 Sun Dira Jihar Imo
A wani rahoton kuma Mataimakin shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima , ya isa jihar Imo da ke Kudu maso Gabashin Najeriya.
Bayanai sun nuna cewa gwamnonin APC 14 sun isa wurin taron, inda za a buɗe shafin yaƙin neman tazarcen gwamnan jihar, Hope Uzodinma, a zabe mai zuwa nan da wata ɗaya.
Asali: Legit.ng