Katsina: Gwamna Radda Ya Kaddamar da Sabuwar Rundunar Tsaro

Katsina: Gwamna Radda Ya Kaddamar da Sabuwar Rundunar Tsaro

  • Malam Dikko Umaru Raɗda ya kaddamar da sabuwar rundunar tsaron al'umma domin tabbatar da zaman lafiya a jihar Katsina
  • Gwamnan ya ce dakarun rundunar zasu ƙara ƙarfafa jami'an tsaro wajen shiga daji da yaƙi da yan bindiga
  • Muhammadu Buhari, gwamnan Dauda Lawal na Zamfara da Abba Gida-Gida na cikin waɗanda suka halarci wurin

Jihar Katsina - Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda, a ranar Talata, ya kaddamar da rundunar 'Community Watch Corps' domin tallafawa kokarin jami’an tsaro na yaki da ‘yan bindiga a jihar.

Kamar yadda ya wallafa a shafinsa na manhajar X, Gwamna Raɗɗa ya nuna farin cikinsa bisa cimma wannan kudiri wanda ya na ɗaya daga cikin alƙawurran da ya ɗauka lokacin kamfe.

Gwamnan Katsina ya kaddamar da sabuwar rundunar tsaro.
Katsina: Gwamna Radda Ya Kaddamar da Sabuwar Rundunar Tsaro Hoto: @Dikko_radda
Asali: Twitter

Yayin da yake kaddamar da rukunin 1 na rundunar, Radda ya ce hakan na cikin kokarin gwamnatinsa na daukar wani tsari na "al'umma" don magance rashin tsaro da ya addabi jihar.

Kara karanta wannan

Murna Yayin Da Tsohon Ministan Buhari Ya Samu Mukami Mai Muhimmanci

Gwamnan ya rubuta a shafinsa cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"A hukumance, na kaddamar da rundunar Katsina Community Watch Corps. Mun samar musu da motocin sulƙe, motocin sintiri domin su gudanar da aikin da ake buƙata."

A sanarwan da mai magana da yawun gwamnan, Ibrahim Kaula, ya fitar, rukunin farko na rundunar ya kunshi matasa 2,400 da aka zabo daga kananan hukumomi 34 na jihar.

Dikko Raɗda ya ce:

“Babbar manufar wannan runduna ita ce haɗin kai, haɗin gwiwa, da mutunta juna. Idan muka yi amfani da ilimin cikin gida da haɓaka amana, ba alamun matsalar kaɗai zamu magance ba, harda tushen matsalar ta tsaro."

Radda ya ce a lokacin da yake yakin neman zaben gwamna, ya ziyarci gunduma 361 da ke jihar, inda ya ga irin illar rashin tsaron da ake fama da shi a sassan Katsina.

Kara karanta wannan

Muhimman Matakai 5 Da Gwamna Abba Ya Dauka Bayan Kotu Ta Kwace Nasararsa a Zabe

A cewarsa, wannan dalili ne ya sanya ya kirkiro wannam runduna wacce za ta sa ido kan lamarin duk a wani bangare na yunkurinsa na kawo ƙarshen ta'addanci.

Manyan jiga-jigan da suka halarci taron a Katsina

Tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, da wasu gwamnonin arewa kamar Dauda Lawal (Zamfara), Ahmad Aliyu (Sokoto), Nasir idris (Kebbi), Abba Kabir (Kano), Mai Mala Buni (Yobe) da Umar Namadi (Jigawa) sun halarci taron.

Arewa maso Gabas na fama da matsalar ta'addancin 'yan bindiga, waɗanda a kai a kai suna kai hari kan fararen hula, su yi garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa.

"Ku Tuba Ko Ku Zarce Lahira" CDS Ya Aike da Sako Ga Yan Ta'adda a Najeriya

A wani rahoton kuma Babban hafsan tsaro na ƙasa (CDS) ya kai ziyarar aiki ga rundunar Operation Haɗin Kai, ya aike da sako ga yan ta'adda.

Janar Christopher Musa ya roƙi 'yan Najeriya su ci gaba da taimaka wa hukumomin tsaro da bayanan sirri don kawo karshen matsalar tsaro.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba Gida-Gida Ya Sanar da Ranar Ɗaura Auren 'Yan Mata da Zawarawa 1,800 a Kano

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262