Dangote Ya Yi Magana Kan Karya Farashin Buhun Siminti Zuwa N2,400

Dangote Ya Yi Magana Kan Karya Farashin Buhun Siminti Zuwa N2,400

  • Kamfanin simintin Dangote ya mayar da martani kan rahotannin yin tallace-tallace da kuma daidaita farashin kayayyakin sa zuwa N2,400
  • An yi ta yaɗa batun rage farashin a shafukan sada zumunta musamman a dandalin WhatsApp
  • Legit Hausa ta tuntuɓi kamfanin Dangote domin tabbatar da shirin tallace-tallacen da ake yayatawa da kuma rage farashin

Kamfanin simintin Dangote, ɗaya daga cikin kadarorin attajirin Najeriya, Aliko Dangote, ya musanta rahotannin da ake yadawa a wasu kafafen sadarwa na yanar gizo (ba Legit.ng ba) dangane da batun yin tallace-tallace da kuma rage farashi.

Kamfanin ya fayyace cewa bai fara wani talla ko sake duba farashin kayansa ba kamar yadda aka yi iƙirari a wata sanarwa ta bogi mai ɗauke da kwanan watan ranar Lahadi, 8 ga watan Oktoban 2023, wacce ta yaɗu a shafukan sada zumunta.

Dangote ya yi magana kan rage farashin siminti
Dangote ya musanta rage fsrashin siminti Hoto: DANCEMENT
Asali: Facebook

Sanarwar wacce aka ce ta fito daga kamfanin ta yi iƙirarin cewa kamfanin simintin na Dangote zai sayar da simintinsa ga jama'a a kan farashin kamfani na naira 2,410 kacal a kan kowane buhu.

Kara karanta wannan

Gowon, Akeredolu Da Wasu Fitattun Yan Najeriya 4 Da Aka Yi Karyan Sun Mutu

Dangote ya mayar da martani kan rage farashi

Da yake mayar da martani, babban jami'in kula da sa hannun jari da sadarwa na rukunin kamfanonin Dangote, Anthony Chiejina, ya bayyana rahotannin a matsayin tsabagen ƙarairayi marasa tushe ballantana makama.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kalamansa:

"Mahukunta kamfanin sun sanar da jami'an tsaro a hukumance da su gano, su bayyana sunaye, da kuma kunyata wadanda suka aikata wannan labarin na yaudara."
"Kamfanin simintin Dangote ya buƙaci kwastomomi da sauran masu ruwa da tsaki da su cigaba da siyan siminti mai inganci tare da yin taka-tsan-tsan da masu damfara, wadanda suka duƙufa wajen ganin sun damfare su kuɗaɗensu."

Ana yawan yaɗa jita-jita kan Dangote

Wannan dai ba shi ne karon farko da wani rahoto na ƙarya kan rage farashin simintin Dangote ya yaɗu shafukan sada zumunta ba.

A wani rahoto da ya gabata, Legit.ng sai da ta tuntuɓi kamfanin Dangote, biyo bayan ikirarin cewa kamfanin zai rage farashin siminti daga N5,500 zuwa N2,700 a ranar 1 ga watan Oktoban 2023, domin murnar samun ƴancin kan Najeriya.

Kara karanta wannan

"Ka dawo da shi N1500": Yan Najeriya Sun Yi Martani Bayan Dangote Ya Musanta Rage Farashin Siminti Zuwa N2,400

Jita-jitar dai ta kara yawaita ne tun bayan da kamfanin BUA ya sanar da rage farashin simintinsa daga N5,500 zuwa N3,000 da N3,500.

BUA Ya Kara Farashin Kayan Abinci

A wani labarin na daban kuma, kamfanin BUA ya sanar da yin ƙari kan farashin kayayyakin abinci da yake samarwa.

Ƙarin kuɗin kayayyakin dai na zuwa ne bayan kamfanin ya rage farashin sari na simintinsa a kasuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng