ECOWAS: Tsohon Jigon APC Ya Bukaci a Kori Tinubu a Matsayin Shugaban Kungiyar

ECOWAS: Tsohon Jigon APC Ya Bukaci a Kori Tinubu a Matsayin Shugaban Kungiyar

  • An buƙaci shugabannin ƙasashen ƙungiyar ECOWAS da su kori shugaban ƙasa Bola Tinubu daga shugabancin ƙungiyar
  • Kwamared Timi Frank ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake mayar da martani kan badaƙalar takardun bogi da ake zargin Shugaba Tinubu ya yi
  • Ya bayyana cewa martabar ƙungiyar da ke yankin Afirika na cikin haɗari, kuma ba za a ɗauki shugabancin Tinubu da muhimmanci ba

FCT, Abuja - A yayin da ake ta cece-kuce kan takardar shaidar kammala karatun shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu daga jami'ar jihar Chicago (CSU), tsohon mataimakin kakakin jam'iyyar APC, Kwamared Timi Frank, ya buƙaci a kore shi daga muƙaminsa na shugaban ƙungiyar ECOWAS.

Frank yayi wannan kiran ne ta wata sanarwa da ya rabawa Legit.ng a Abuja a ranar Talata, 10 ga watan Oktoba.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar Labour Party Ta Bayyana Dalili 1 Rak Da Ya Sa Peter Obi Ba Zai Yi Aiki Da Gwamnatin Tinubu Ba

Timi Frank ya bukaci a kori Tinubu daga shugabancin ECOWAS
Shugaba Tinubu a wajen taron ECOWAS Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Meyasa Frank yake son a kori Tinubu?

A cewar sanarwar, Frank yana kira ne da a kori Tinubu daga muƙaminsa na shugaban ECOWAS saboda gano cewa ya yi jabun satifiket wanda ya miƙa wa hukumar zabe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) domin tantance shi a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kalamansa:

"Idan ECOWAS na son a cigaba da damawa da ita kuma ta riƙe mutuncinta da mutuntawa a tsakanin ƙasashe mambobinta, musamman wajen tunkarar gwamnatin mulkin soja da ke yaɗuwa cikin sauri kamar annoba a fadin yankin, dole ne ta yi sauri don kare mutuncinta."

Hakazalika Frank yayi kira ga shugabannin ƙasashen kungiyar ECOWAS na baya da na yanzu da su sanya ƙungiyar ta yi abin da ya dace ta hanyar zaɓen shugaba na riƙon ƙwarya har zuwa lokacin da za a tabbatar da shi a zaman taron ƙungiyar na gaba.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Shugaba Tinubu Ya Yi Sabbin Nade-Nade 5 Masu Muhimmanci

Ya ce rashin ɗaukar matakin da ya dace zai sanya ƙungiyar a wani matsayi mara daɗi wanda ba za a mutunta duk wani hukunci da aka cimmawa a lokacin mulkin Tinubu ba.

LP Ta Ce Obi Ba Zai Yi Aiki Da Tinubu Ba

A wani labarin kuma, jam'iyyar Labour Party (LP) ta bayyana cewa ɗan takarar shugaban ƙasarta ba zai yi aiki da gwamnatin Shugaba Tinubu ba.

LP ta ce a yanzu Peter Obi ya mayar da hankali wajen ƙwato nasararsa da aka sace a kotun ƙoli.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng