'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Daibai Jami'ar Jihar Nasarawa
- 'Yan bindiga sun yi garkuwa da ɗalibai huɗu na jami'ar jihar Nasarawa da ke Keffi ranar Litinin da daddare
- Hukumar makarantar ta tabbatar da faruwar lamarin, tana mai cewa jami'am tsaron jami'ar da hukumomin tsaro na kokarin ceto ɗaliban
- Kakakin rundunar 'yan sanda reshen jihar Nasarawa, DSP Rahman Nansel, ya ce tuni suka fara farautar maharan domin ceto ɗaliban
Jihar Nasarawa - Wasu miyagun 'yan bindiga sun yi awon gaba da ɗalibai huɗu na jami'ar jihar Nasarawa da ke Keffi ranar Litinin da daddare.
Jaridar Vanguard ta tattaro cewa 'yan bindigan sun sace ɗaliban da misalin ƙarfe 10:30 na dare lokacin da suka kai farmaki Anguwan Ka'are, ƙaramar hukumar Keffi.
Ɗaliban da maharan suka yi garkuwa da su sun haɗa da, Rahila Hanya, Josephine Gershon, Rosemary Samuel, da kuma Goodness Samuel, duk 'yan aji ɗaya watau 100 Level.
Jam'iyyar Labour Party Ta Bayyana Dalili 1 Rak Da Ya Sa Peter Obi Ba Zai Yi Aiki Da Gwamnatin Tinubu Ba
Hukumar jami'a ta yi magana kan lamarin
Yayin da aka tuntuɓe shi, jami'in hulɗa da jama'a na jami'ar, Abraham Ekpo, ya ce hukumar makaranta ta samu labarin garkuwa da ɗalibanta da 'yan bindiga suka yi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce jami’an tsaron cikin jami'ar jihar Nasarawa na aiki ƙafaɗa da kafaɗa da sauran hukumomin tsaro domin ganin an ceto ɗaliban cikin ƙoshin lafiya.
Wane mataki jami'an tsaro suka ɗauka?
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Ramhan Nansel, ya tabbatar da lamarin ga Channels tv ta wayar tarho ranar Talata.
Ya ce da sanyin safiyar ranar Talata ne rundunar ‘yan sandan jihar ta samu kiran gaggawa cewa wasu ‘yan bindiga sun kai farmaki wani gida a Angwan Ka'are.
“Hukumar 'yan sanda ta samu labari da misalin karfe 12:55 na safe, bayan wani kiran gaggawa cewa yan bindiga sun kutsa wani gida da ke Angwan Ka'are, Keffi sun sace mutane."
"Dakarun 'yan sanda da haɗin guiwar jami'an sojoji sun kai ɗauki inda suka kewaye Anguwar, amma bisa rashin sa a ba su tarad da maharan ba."
“Kwamishanan ‘yan sanda ya bada da umarnin farautar maharan da nufin ceto wadanda lamarin ya rutsa da su ba tare da sun ji rauni ba.”
Matar Gwamnan APC Ta Ci Gaba da Ƙoyarwa a Jami'ar Jihar Ekiti
A wani labarin kuma Matar gwamnan jihar Ekiti mai ci ta zama abin kwatance yayin da ta koma aji ta ci gaba da karantar da ɗaliban jami'ar EKSU.
Dokta Olayemi Oyebanji, ta ce zata ci gaba da ware lokaci duk da yawan ayyukan da ke gabanta, ta riƙa karantarwa a jami'ar.
Asali: Legit.ng