Majalisar Jihar Kano Ta Bai Wa Auwalu Mai Adaidaita Sahu Naira Miliyan 1.5 Da Lambar Yabo
- Har zuwa yau, mai adaidaita sahu, Auwalu Salisu na ci gaba da karbar kyaututtuka da yabo daga al'umma
- Majalisar jihar Kano ta bai wa Dan Baba kyautar makudan kudade har Naira miliyan 1.5 don kara masa karfin gwiwa
- Auwalu Salisu dai shi ne wanda ya mayar da Naira miliyan 15 ga wani dan Chadi da ya manta kudaden a cikin adaidaita sahunsa
Jihar Kano - Majalisar dokokin jihar Kano ta bai wa Auwalu Salisu kyautar Naira miliyan 1.5 bayan mayar da makudan kudade da aka bari a adaidaita sahunsa.
Mai adaidaita sahun, Auwalu Salisu ya mayar da Naira miliyan 15 na wani dan Chadi da ya manta su a cikin adaidaita sahu.
Yaushe majalisar ta gwangwaje Auwalu da kudaden a Kano?
Majalisar a zamanta na yau Litinin 9 ga watan Oktoba ta bai wa Salisu kyautar kudin wanda mambobin su ka hada don kara masa karfin gwiwa.
Kano: Abba Gida Gida Ya Amince Da Biyan Makudan Kudade Ga Daliban Da Ke Jami'o'in Najeriya, Ya Bayyana Dalili
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban majalisar ya ce Salisu ya zama daban a cikin al'umma inda ya mayar da wadannan makudan kudade ga mai su, Tribune ta tattaro.
Majalisar ta kuma ba shi takardar karramawa inda ta bukaci gwamnatin jihar ta dauki nauyin karatunshi har zuwa Jami'a.
Wane martani Auwalu ya yi ga majalisar a Kano?
Da ya ke martani, mai adaidaita sahun, Dan Baba ya nuna godiyarshi ga majalisar da irin wannan karramawa da su ka masa.
Ya ce ba zai taba mantawa da wannan karamci ba inda ya yi addu'a ga majalisar wurin gudanar da ayyukansu cikin nasara.
A kwanakin baya ne majalisar dokokin jihar Kano ta gayyaci Auwalu Salisu, direban adaidaita sahu da ya mayar da makudan kudade ga mai su a jihar, Daily Trust ta tattaro.
Majalisar dokokin jihar Kano ta gayyaci direban adaidaita sahu
A wani labarin, majalisar dokokin jihar Kano ta gayyaci Auwalu Salisu, direban adaidaita sahu da ya mayar da makudan kudade ga mai su a jihar.
Wasu daga cikin mambobin majalisar ne su ka kawo wannan kuduri na gayyatar Salisu tare da masa alkawarin kudi.
Wannan na zuwa ne bayan Auwalu ya mayar da Naira miliyan 15 da aka manta a adaidaita sahunsa na wani dan kasar Chadi.
Asali: Legit.ng