Shugabancin Tinubu Ne Daidai da Najeriya, in Ji Jigon APC Kuma Sanata, Sani Musa

Shugabancin Tinubu Ne Daidai da Najeriya, in Ji Jigon APC Kuma Sanata, Sani Musa

  • Sanata a Najeriya ya bayyana cewa, shugabancin Tinubu ya yi daidai da abin da ake bukata a Najeriya
  • Ya kuma kushe yadda Najeriya ta gaza tabuka komai a cikin shekaru 63 da ta yi da samun 'yancin kai
  • Sanatan ya yi tsokaci ga yadda kasar nan ke fama da dawainiyar tafiyar da harkar man fetur tsawon lokaci

FCT, Abuja - Shugaban Kwamitin Kudi na Majalisar Dattawa, Sanata Sani Musa (APC daga Neja ta Gabas), ya bayyana gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu a matsayin jagoranci na-gari da kasar ke bukata a wannan lokaci.

Sanata Musa ya bayyana hakan ne a Abuja ranar Asabar a lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai a bikin cikar Najeriya shekaru 63 da samun ‘yancin kai.

Sai dai ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta mayar da wasu matatun man fetur din da ta mallaka ga 'yan kasuwa, rahoton jaridar The Nation.

Kara karanta wannan

Atiku Ya Yi Kira Ga Kwankwaso Da Peter Obi Su Hada Kai Da Shi Don Cire Tinubu, Ya Bada Dalili

Tinubu ne ya dace da mulkin Najeriya
Tinubu ne daidai da mulkin Najeriya | Hoto: KOLA SULAIMON/AFP
Asali: Getty Images

A cewarsa, matatun man basu tsinanawa Najeriya komai ba duba da kudaden da ake kashewa wajen kulawa da kuma gyara su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bamu tabuka komai ba cikin shekaru 63

Ya kara da cewa Najeriya ba ta tabuka komai ba a cikin shekaru 63 da ta 'yancin kai, saidai, ya bayyana cewa abin da take bukata a yanzu shi ne shugabanci na kwarai.

Shugabancin da ya dace, in ji shi, zai taimaka wajen amfanar dumbin albarkatun yawan mutane da na kasa da aka albarkaci Najerya da su, rahoton Leadership.

Daga nan, ya dage cewa gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta nuna kwazo da aiki daidai da irin shugabancin da kasar nan ke bukata.

'Yan jam'iyyun adawa na ci gaba da bayyana kokensu ga yadda gwamnatin Tinubu ke ci gaba da kawo tsarukan da ke jefa 'yan Najeriya a wahala.

Kara karanta wannan

Dan Kasuwa A Kano, Dantata Ya Kirkiro Bankin Yanar Gizo Da Zai Yi Gogayya Da Opay, Kuda, Ya Dauki Alkawari

Tinubu ya kori N-Power, zai dauki ma'aikata

A wani labarin, gwamnatin tarayya ta kashe shirin N-Power zai samar da aikin yi ga matasa miliyan biyar nan da shekaru biyar masu zuwa a kasar nan, The Nation ta ruwaito.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Manajan shirye-shirye na N-Power, Akindele Egbuwalo ya fitar.

Egbuwalo, wanda ya bukaci ‘yan Najeriya su fahimci dalilin kashe shirin da kuma sake fasalin da ake yi, ya ce gwamnatin tarayya na kokarin kawo tsari mai kyau a shirin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.