Gwamnatin Tarayya Ta Yi Karin Haske Kan Dalilan Dakatar Da Shirin N-Power

Gwamnatin Tarayya Ta Yi Karin Haske Kan Dalilan Dakatar Da Shirin N-Power

  • Gwamnatin tarayya ta fito ta yi ƙarin haske kan dalilin da ya sanya ta dakatar da shirin tallafawa matasa na N-Power
  • FG ta hannun ministan jinƙai da walwala, Dr. Betta Edu ta bayyana cewa akwai buƙatar a gudanar da bincike kan yadda aka tafiyar da shirin
  • Edu ta kuma ƙara da cewa za a ƙara faɗaɗa shirin ta yadda matasa miliyan biyar za su riƙa cin gajiysrsa

FCT, Abuja - Ƙarin dalilan da suka sanya aka dakatar da shirin gwamnatin tarayya na N-Power sun fito.

Shirin N-Power na daya daga cikin shirye-shiryen da gwamnatin da ta shuɗe ta bullo da su domin ƙarfafawa matasa gwiwa.

Gwamnatin tarayya ta bayyana dalilin dakatar da N-Power
Gwamnatin tarayya ta fadi dalilin dakatar da N-Power Hoto: Dr Betta Edu, Npower, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Ministar harkokin jin kai da yaki da fatara, Betta Edu ta sanar da dakatar da shirin a ranar Asabar yayin wata hira da aka yi da ita a gidan talabijin.

Kara karanta wannan

Yan Ta'adda Sun Kai Sabon Farmaki a Jihar Arewa, Sun Yi Awon Gaba Da Manoma Masu Yawa

Edu, a yayin tattaunawar, ta bayyana cewa an yanke shawarar dakatar da shirin ne saboda wasu kurakurai da ke cikin shirin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai, a wata sanarwa da ministar ta fitar a ranar Lahadi, 8 ga watan Oktoba, ta yi karin haske kan dakatar da shirin, cewar rahoton The Nation.

Meyasa FG ta dakatar da N-Power?

Ta bayyana cewa bincike ya nuna cewa wasu masu kula da shirin na riƙe da kuɗaɗen matasan da ke amfani da shirin, kuma kwantiraginsu ta ƙare a watan Maris na 2023 ba tare da sabunta komai ba.

Ministar ta kuma bayyana cewa wasu da suka ci gajiyar tallafin suna yin wasu ayyuka amma har yanzu suna cin gajiyar shirin, yayin da wadanda suka yi aiki da gaske ba a biya su ba.

Ta kuma ce an dakatar da shirin ne saboda akwai bukatar a tantance adadin mutanen da ke cikin shirin, da waɗanda suka fice daga shirin, da wadanda suke bin basussuka, ko sun je wuraren aiki ko ba su je ba, da kuma yadda aka yi amfani da kudade a kan shirin.

Kara karanta wannan

"Ku Shirya Rusa Kuri'un Ku a 2023": Martanin Yan Najeriya Bayan Gwamnatin Tinubu Ta Dakatar Da Shirin N-Power

Dalilan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun manajan shirye-shirye na N-Power, Dr. Akindele Egbuwalo a madadin ministar.

Za a faɗaɗa N-Power

Ministan ta kuma ce za a faɗaɗa shirin domin ɗaukar ƴan Najeriya miliyan biyar nan da shekaru biyar masu zuwa.

Baya ga haka, ta kuma ce za a sake duba ɓangaren ƙayyade shekarun masu cin gajiyar shirin zuwa shekaru 18-40 saɓanin yadda tsarin yake a baya na 18-35.

Martanin Yan Najeriya Ƙan Dakatar Da N-Power

A wani labarin kuma, ƴan Najeriya da dama sun nuna takaicinsu kan dakatar da shirin N-Power da gwamnatin tarayya ta yi.

Da yawa daga cikinsu sun nuna cewa shirin yana taimakawa matasa da dama su dogara da kansu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng