Yan Ta'adda Sun Sace Manoma 30 a Jihar Kaduna a Wani Sabon Hari
- Miyagun ƴan ta'adda sun sake kai mummunan hari a ƙaramar hukumar Chikun ta jihar Kaduna
- Ƴan ta'addan a harin da suka kai a ƙauyen Chikuri sun yi awon gaba da manoma sama da mutum 30 suna cikin neman na abinci
- Mazauna yankin sun koka kan yadda ƴan ta'addan suka addabi yankinsu, wanda hakan ya sanya suna rayuwa cikin tashin hankali da baƙin ciki
Jihar Kaduna - Wasu ƴan ta'adda sun yi garkuwa da manoma sama da 30 da sanyin safiyar ranar Asabar, 7 ga watan Oktoba a ƙauyen Chikuri da ke ƙaramar hukumar Chikun a jihar Kaduna.
Wani mazaunin garin mai suna Dogara Peter, wanda ya tabbatar wa da jaridar Punch aukuwar lamarin, ya ce mahaifiyarsa da ƴar uwar sa na cikin waɗanda abin ya shafa.
A cewarsa, an sace mutanen ne a lokacin da suke aiki a Maikudi Farms.
A kalamansa:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Al’ummarmu sun shiga ruɗani saboda har yanzu ƴan ta'addan da suka yi garkuwa da su ba su tuntuɓemu ba. Muna son jami’an tsaro da gwamnati su zage damtse wajen ganin mutanenmu sun dawo cikin ƙoshin lafiya."
Peter ya koka da cewa lamarin na baya-bayan nan shi ne karo na uku da aka yi garkuwa da mutane a cikin iyalansa, inda ya ce lamarin ya gurgunta iyalansa ta fuskar tattalin arziki.
"Ba mu da inda za mu nemo abin da za mu biya kuɗin fansa da shi. Al'ummar gaba ɗaya sun shiga cikin tashin hankali da baƙin ciki. Fatanmu na ƙarshe yana ga hukumomin tsaro da gwamnati."
Me ƴan sanda suka ce dangane da harin?
Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan jihar Kaduna, Mansir Hassan, bai amsa kiran da aka yi masa a waya.
Har ila yau bai dawo da amsar saƙon da akaa tura masa ba ta wayarsa, har ya zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton.
Yan Bindiga Sun Halaka Mutum 4
A wani labarin kuma, ƴan bindiga sun kai sabon hari a unguwar Dankaƙi cikin ƙaramar hukumar Zariya a jihar Kaduna.
Ƴan bindigan sun halaka mutum huɗu tare da yin awon gaba da wasu mutum biyar a yayin harin.
Asali: Legit.ng