Yan Najeriya Sun Yi Martani Bayan FG Ta Dakatar Da N-Power
- Bayan shekaru da yawa da yin rukunoni uku, gwamnatin tarayya ta dakatar da shirin N-Power har sai baba-ta-gani
- Ministar harkokin jin kai da yaƙi da talauci, Betta Edu, ta sanar da dakatarwar a ranar Asabar, 7 ga watan Oktoba
- A halin da ake ciki, ministar ta ce gwamnati ta ƙaddamar da bincike kan yadda aka yi amfani da kuɗaɗen shirin tun farkonsa
FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayyar Najeriya a ranar Asabar, 7 ga watan Oktoba, ta sanar da dakatar da shirin N-Power sai baba-ta-gani.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito cewa shirin N-Power ya kasance a ƙarƙashin ma'aikatar jin ƙai, walwala da yaƙi da talauci.
FG ta dakatar da shirin N-Power
Betta Edu, ministar kula da ayyukan jin kai da rage raɗaɗin talauci, ta sanar da dakatar da shirin yayin wata tattaunawa da ta yi da gidan talabijin na Continental (TVC).
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Beta ta ce dalilin rusa shirin bai rasa nasaba da matsalolin da ke cike a shirin wanda aka samu a gwamnatin da ta shude.
Ministar ta ce sun fara binciken yadda wasu kudade su ka bace a shirin tun bayan fara aiwatar da shirin.
Ƴan Najeriya sun yi martani
Bayan sanar da hakan, wasu masu amfani da kafofin sada zumunta sun yi martani kan dakatar da shirin.
Legit.ng ta tattaro wasu daga ciki waɗanda aka yi a shafin X (wanda a baya aka fi sani da Twitter).
Ga kaɗan daga ciki nan ƙasa:
@Alex_slimxx ya rubuta:
"Ya ɗauki lokaci mai yawa fiye da yadda ake tsammani."
@1Akadri ya rubuta:
"Hakan ya yi kyau."
@LokritWen ya rubuta:
"Ya ku ƴan Npower, ku kasance a shirye don sake fasalin ƙuri'un ku a 2027. Kada ku manta da wannan cikin gaggawa!"
@Muhammad9740614
"Najeriya kasa ce mai arziki Najeriya kasa ce mai arziki BlaBla amma kawai biyan npower wani abu ne daban. Mtchew"
Mutum Miliyan 1 Sun Rasa Madafa
A wani labarin kuma, dakatar da shirin N-Power da gwamnatin shugaban ƙasa Bola Tinubu, ta yi ta jefa matasa da dama cikin halin rashin madafa.
Sama da matasa miliyan ɗaya ne dai masu amfani da shirin za su rasa hanyoyin samun kuɗaɗen shiga a dalilin dakatar da shirin.
Asali: Legit.ng