Umahi Da Geidam Ba Su Yi Murabus Daga Mukamin Sanatoci Ba

Umahi Da Geidam Ba Su Yi Murabus Daga Mukamin Sanatoci Ba

  • Biyu daga cikin ministocin shugaban ƙasa Bola.Ahmed Tinubu ba su yi murabus daga muƙaminsu na sanatoci ba
  • David Nweze Umahi da Ibrahim Geidam ba su aike takardar murabus ɗinsu zuwa ga majalisar dattawan ba
  • Kakakin majalisar dattawa ya bayyana cewa har yanzu kujerunsu na nan a majalisar tun da ba su aike da takardar murabus ba

FCT, Abuja - Kwanaki 46 bayan rantsar da su a matsayin ministoci da shugaban ƙasa Tinubu ya yi, ministan ayyuka, David Umahi, da kuma ministan harkokin ƴan sanda, Ibrahim Geidam, ba su yi murabus daga muƙaminsu na sanatoci ba, cewar rahoton The Punch.

Umahi, tsohon mataimakin shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa wanda ke wakiltar Ebonyi ta Kudu, da Geidam wanda yake wakiltar Yobe ta gabas suna cikin ministoci 48 a majalisar ministocin Tinubu da aka rantsar a ranar 21 ga watan Agusta.

Kara karanta wannan

Mummunan Ibtila'i Ya Laƙume Rayukan Mutum 6 a Babban Titin Kaduna Zuwa Abuja

Umahi da Geidam ba su yi murabus daga mukamin sanatoci ba
Umahi Da Geidam na cigaba da zama sanatoci Hoto: Ibrahim Geidam, Engr. David Nweze Umahi
Source: Facebook

Shi dai tsohon gwamnan na jihar Ebonyi ya samu naɗin nasa ne wata guda bayan da aka nada shi a matsayin babban jami’i a majalisar dattawa ta 10, yayin da Geidam wanda kuma tsohon gwamnan jihar Yobe ne yake cikin wa'adi na biyu a matsayin sanata.

Meyasa har yanzu kujerunsu suke a majalisa?

Da yake mayar da martani kan dalilin da ya sa har yanzu ba a bayyana kujerunsu a matsayin wanda babu kowa a kai ba, kakakin majalisar dattawa, Yemi Adaramodu, ya bayyana cewa har yanzu tsaffin ƴan majalisar ba su aika da takardar murabus ɗinsu ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce ba zai taɓa yiwuwa majalisar dattawa ta bayyana kujerun a matsayin wanda babu kowa a kansu ba tunda har yanzu ba su aika da murabus ɗinsu ba.

"Majalisar dattijai ba za ta iya bayyana kujera a matsayin wacce babu kowa a kanta ba idan babu wata magana daga tsaffin ƴan majalisar dangane da murabus ɗin nasu. Akwai hanyoyi da ake bi wajen yin hakan."

Kara karanta wannan

Babbar Matsala 1 Da Aka Gano Bayan Taron da Atiku Ya Gudanar Kan Shugaba Tinubu a Abuja

"A lokacin da suka aika da saƙon nasu ne shugaban majalisar dattawa zai karanta saƙon a zaman majalisa, inda a lokacin za a iya bayyana kujerun a matsayin babu kowa a kansu."

Adaramodu ya ƙara da cewa:

"Idan da akwai wata sanarwa daga gare su, na tabbata da shugaban majalisar dattawa ya karanta wa ƴan Najeriya."

Dantata Da AA Rano Sun Samu Kwangila

Ku na da labari cewa Sayyub Dantata da AA Rano sun kwangiloli masu tsoja daga kamfanin man fetur na ƙasa (NNPC).

Attajiran biyu tare da wasu attajirai biyu sun samu kwangilar tsaftace bututun man fetur a faɗin ƙasar nan ta hannun kamfanoninsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng