An Kama Malami da Dillali Kan Zargin Sayar da Filayen Bakin Titi a Abuja
- Jami'an tsaro sun kama Malamin Coci da wani mutum ɗaya bisa zargin damfarar mazauna haramtattun gine-gine a Abuja
- Rahoto ya nuna waɗan da ake zargin sun fara karɓan kuɗaɗe daga mutanen don kare su daga rusau
- Kwamishinan 'yan sandan Abuja ya bada umarnin gudanar da bincike mai zurfi gabanin gurfanar da su a Kotu
FCT Abuja - Jami’an tsaro da ke aiki a babban birnin tarayya Abuja sun kama wasu mutane biyu da ake zargi da satar fili, Yusuf Garba Ibrahim wanda ake kira Baba Khalifa da Fasto Emmanuel Ayisa.
Rahoton Daily Trust ya ce an kama mutanen biyu bisa zargin karɓan ƙudaɗe daga wasu mutane a kewayen wasu haramtattun gine-gine da matsugunai a Jahi da Kado.
An tattaro cewa ana ci gaba da tafka ta’asa ba bisa ka’ida ba a kan titin da ke tsakanin unguwannin Kado da Jahi a birnin Abuja, inda aka dade da jingine aikin titin.
Tawagar rundunar hadin gwiwa ta Abuja ne suka yi wannan kame jiya biyo bayan samun bayanan sirri da ke nuna mutane na harhaɗa wa waɗan da ake zargi kuɗaɗe.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda asirin Fasto da mutumin ya tonu
Sakataren rundunar haɗin guiwa ta FCTA, Peter Olumuji, ya ce jami'an tsaro sun tattara bayanan leƙen asiri cewa masu haramtattun gine-gine da tantuna suna haɗa wa wasu kuɗi.
Bayanan sun nuna cewa mutanen suna haɗa kuɗin ne domin tsira daga shirin risau da ma'aikatar Abuja zata yi.
Nan da nan jami'an tsaro suka zaƙulo ainihin waɗanda ake haɗa wa kuɗin kuma suka garzaya suka cafke su.
Olumuji ya bayyana cewa kwamishinan ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja ya ba da umarnin a gudanar da cikakken bincike kafin a gurfanar da su gaban kuliya.
Ya ce:
"Hukunta su zai zama darasi ga masu damfarar mutane waɗanda shirin rusau zai shafa a Anguwannin, wannan abu ne da FCTA ba zata lamurta ba."
Primeboy Ya Mika Kansa Ga Yan Sanda Bayan Ayyana Nemansa Ruwa a Jallo
A wani rahoton kuma Primeboy, abokin fitaccen mawaƙin nan da ya mutu Mohbad ya miƙa kansa ga rundunar yan sandan jihar Legas.
Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar, Benjamin Hundeyin, shi ne ya tabbatar da haka a wata sanarwa da ya wallafa a.shafinsa na manhajar X.
Asali: Legit.ng