Gwamna Abidoun Ya Ɗauki Sabbin Malamai 1,000 Aiki a Gwamnatin Ogun
- Gwamna Dapo Abiodun ya ce gwamnatinsa ta ɗauki sabbin malamai 1,000 aiki a makarantu gwamnati na jihar Ogun
- Ya ce wannan wani ɓangare ne na yunƙurin inganta fannin ilimi da walwalar malamai
- Gwamnan ya kuma tabbatar da cewa akwai sabbin gyare-gyare da zai yi wa ɓangaren ilimi wanda ya ƙunshi ɗaukar malamai masu neman kwarewa
Jihar Ogun - Gwamnatin jihar Ogun ta sanar da cewa ta dauki sabbin malamai 1,000 aiki a makarantun gwamnati a wani yunƙuri na inganta koyo da koyarwa.
Gwamna Dapo Abiodun na Ogun ne ya faɗi haka ranar Alhamis a wurin bikin ranar malamai ta duniya da aka gudanar a dakin taro na Obas Complex da ke Abeokuta.
Abiodun ya kuma tabbatar wa malaman makaranta cewa zai ƙara yi wa ɓangaren ilimi gyara domin inganta koyo da koyarwa, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.
Ya ce:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Mun amince da ba da takardar ɗaukar aiki ta dindindin 1000 ga wasu malamai a Ogun, waɗanda suka nuna ƙwarewar su a lokacin gwajin da aka musu na shekaru biyu."
"Muna ƙara miƙa tsantsar godiyarmu ga shugabanni da mambobin ƙungiyoyin malamai NUT, ASUS da AOPSHON saboda sadaukarwar da suke yi."
Zamu ɗauki ƙarin malamai 2,000 aiki - Abiodun
Gwamnan ya ƙara da bayanin cewa jihar Ogun zata ƙara ɗaukar malamai masu neman ƙwarewa 2,000, wanda ƙari ne daga 2,000 da aka ɗauka tun da farko.
A cewarsa, hakan wani ɓangare ne na kokarin cike giɓin malamai da kuma cika alƙawarin da ya ɗauka a jihar Ogun, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Ya shaida wa mahalarta taron cewa: “Muna so mu tabbatar wa duk masu ƙoƙarin gina kasa cewa za mu ci gaba da jajircewa wajen inganta walwala da jin dadin malamai."
"Haka zalika, muna sa ran su ci gaba da bada gudummuwa wajen ci gaban fannin ilimi, domin ta hanyar hadin gwiwarmu ne za mu iya samar da makoma mai albarka."
Tsohuwar Mai Tsawatarwa a Majalisar Wakilai, Binta Bello, Ta Fice Daga PDP
A wani rahoton kuma Fatima Binta Bello, 'yar majalisar da ta wakilci mazabar Kaltungo/Shongom a majalisar wakilan tarayya ta 8 ta fice daga PDP.
Tsohuwar mai tsawatarwa ta marasa rinjaye a majalisar wakilai ta tabbatar da haka ne a wata wasiƙa da ta fito ranar Alhamis, 5 ga watan Oktoba.
Asali: Legit.ng