Mohbad: Primeboy Ya Mika Kansa Ga Yan Sanda Bayan Ayyana Nemansa Ruwa a Jallo
- Primeboy, abokin fitaccen mawaƙin nan da ya mutu Mohbad ya miƙa kansa ga rundunar yan sandan jihar Legas
- SP Benjamin Hundeyin, mai magana da yawun rundunar ya ce tuni aka tsare shi domin amsa wasu tambayoyi
- Wannan na zuwa ne bayan 'yan sanda sun ayyana nemansa ruwa a jallo tare da saka ladan N1m ga duk wanda ya nuna inda yake
Jihar Lagos - Owodunni Ibrahim wanda aka fi sani da Primeboy wanda ake nema ruwa a jallo kan mutuwar Oladimeji Aloba watau Mohbad ya mika kansa ga ‘yan sanda.
Wannan na zuwa ne bayan rundunar 'yan sanda reshen jihar Legas ta ayyana nemansa ruwa a jallo kuma ta sanya ladan Naira miliyan ɗaya ga duk wanda ya taimaka.
Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar, Benjamin Hundeyin, shi ne ya tabbatar da haka a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na manhajar X.
Ya ce rundunar ta ɗauki wannan mataki ne bayan Primeboy, wanda abokin mawaƙi Mohbad ne tun na yarinta, ya ƙi amsa gayyatar da aka masa kan mutuwar mawaƙin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An samu wasu rahotanni da ba a tabbatar da su ba cewa Primeboy ya bugi marigayin da wani abu mai kaifi a lokacin da wata sa'insa ta shiga tsakaninsu.
Primeboy ya miƙa kansa ga 'yan sanda
Da yake ƙarin haske kan lamarin ranar Alhamis, kakakin 'yan sandan ya bayyana cewa:
"Bayan ayyana nemansa ruwa a jallo, Owodunni Ibrahim Oluwatosin, watau Primeboy ya mika kan sa, inda nan take aka tsare shi domin yi masa tambayoyi da sauran matakan da suka dace."
“Rundunar ‘yan sandan jihar Legas na ƙara tabbatar wa ‘yan uwa, abokai, masoyan Mohbad da sauran jama’a cewa babu wani abin da za a bari wajen tabbatar da gudanar da bincike mai zurfi."
"Haka nan kuma hukumar 'yan sanda ta ba da tabbacin cewa duk mutanen da aka samu da hannu a mutuwar Mista Ilerioluwa Aloba watau Mohbad, za a gurfanar da su gaban kuliya."
Ɗan Majalisar Tarayya, Abdullahi Balarabe, Ya Bukaci A Ba Mutane Damar Kare Kansu
A wani rahoton na daban kuma Ɗan majalisar Bakori da Danja a zauren Majalisar Wakilai, Abdullahi Balarabe Dabai ya bayyana yadda za a magance matsalolin tsaro.
Honorabul A. B Dabai ya bukaci gwamnati ta bai wa al'umma damar kare kawunansu ta hanyar sanya idanun jami'an tsaro.
Asali: Legit.ng