“Ina Karbar Albashi N998k Duk Wata a Aikin Wanke Gawa”: Matashiya Da Ke Zaune a Turai Ta Magantu

“Ina Karbar Albashi N998k Duk Wata a Aikin Wanke Gawa”: Matashiya Da Ke Zaune a Turai Ta Magantu

  • Wata yar TikTok mai suna Sexydiva, wacce ke aiki a matsayin ma'aikaciyar dakin ajiyar gawa a Belgium, ta bayyana cewa tana karbar albashi GH¢86,000 (N998,438.50) duk wata
  • A cewarta, koda dai ana biya sosai a aikin, yana da matukar wahala domin ta kan tsaftace kimanin gawarwaki biyar a kullun
  • Ta bayyana a cikin bidiyon da ZionFelix ya wallafa a Facebook cewa aikin yana bukatar karfin hali da tsaftatacciyar zuciya

Wata yar TikTok daga kasar Ghana mai suna Sexydiva, wacce ke aiki a matsayin ma'aikaciyar dakin ajiyar gawa a Belgium, ta bayyana a wata hira da ZionFelix cewa tana karbar albashi GH¢86,000 (N998,438.50) duk wata.

Ta bayyana cewa aikinta a kullun ya hada da gyara gawarwaki kimanin guda biyar, tana mai nanata cewa aikin na bukatar karfin gwiwa da rashin tsoro.

Kara karanta wannan

Kungiyar NLC Ta Fadi Yawan Mafi Karancin Albashi Da Za Su Tattauna Da Gwamnati, Ta Yi Wa Ma'aikata Albishir

Sexydiva ta ce tana karbar albashi mai tsoka a aikin wanke gawa a Belgium
“Ina Karbar Albashi N998k Duk Wata a Aikin Wanke Gawa”: Matashiya Da Ke Zaune a Turai Ta Magantu Hoto: @sexydiva via TikTok, ZionFelix via Facebook
Asali: UGC

Sexydiva ta kara da cewar, "idan kai ba irin mutanen nan masu tsaftattaciyar zuciya bane, ba za ka iya yin aikin ba."

Sexydiva ta magantu kan aikin da take yi a Belgium

Hirar wacce ZionFelix ya wallafa a dandalin Facebook, ya haddasa cece-kuce tsakanin yan kasar Ghana da dama, inda suka magantu kan kalubalen da ke tattare da aikin nata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Victor Owusu ya yi martani:

"Sirrin yin nasara a dukkan ayyukanku shine son aikin da ka tsinci kanka a ciki, ku manta da bangaren kudin da farko, da kyau kuma za a samu nasara a karshe. Wannan shine sirrinta!"

Kwame Oteng ya ce:

"Hira mai girma. Ina kaunarta, ita mutum ce, mai tsayin daka, karfi da zuciya mai kyau. Sannu da aiki kafar sadarwa ta Zionfelix.

Maurice Nana Acheampong ta ce:

Kara karanta wannan

Faston Najeriya Fabian Nna Ya Tayar Da Matacce? Gaskiya Ta Bayyana

"Mace mai jarumta, wacce ta kware a kan aikinta. Allah ya yi maki albarka."

Sunshine De Eiish Queen ta ce:

"Kwazon aiki ya cancanci biya mai kyau."

Matashiya ta haddasa cece-kuce saboda yanayin kitsonta

A wani labari na daban, wata matashiyar budurwa ta dauka hankali sosai yayin da ta baje kolin kitsonta wanda yake daya tamkar da dubu.

Kitson wanda ya yi kama da ta daura kwando a ka ya ja hankalin masu tafiya a cikin wata kasuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng