Gwamnan Jihar Osun Ya Sake Sanya Dokar Kulle a Wasu Kananan Hukumomi 2 Na Jihar
- Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun ya sake sanya dokar hana fita a wasu ƙananan hukumomi guda biyu na jihar
- Aɗeleke ya sanya dokar hana fitan ne biyo bayan rikicin filaye da ya sake ɓarkewa a tsakanin al'ummomin ƙauyukan Ilobu da Ifon
- Sanarwar sanya dokar hana fitan wacce ta fito ta hannun kwamishinan watsa labarai na jihar, ta ce dokar ta koma daga ƙarfe 6:00 na dare zuwa ƙarfe 6:00 na safe
Jihar Osun - Gwamnatin jihar Osun ta sanya sabuwar dokar hana fita a ƙananan hukumomin Irepodun da Orolu na jihar, biyo bayan rikicin ƙabilanci tsakanin al'ummar ƙauyukan Ilobu da Ifon.
Idan dai za a iya tunawa gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ya sanya dokar hana fita a ƙananan hukumomin biyu a farkon watan Satumba, bayan da aka samu rikici tsakanin ƙauyukan biyu.
Daga baya an sassauta dokar hana fita bayan hankula sun kwanta a yankin, rahoton Tribune ya tabbatar.
Meyasa aka sake sanya dokar?
Sai dai, wata sanarwa da Kolapo Alimi, kwamishinan watsa labarai da wayar da kan jama’a na jihar, ya fitar a ranar Laraba, ta ce Adeleke ya bayar da umarnin a mayar da dokar hana fita a ƙananan hukumomin biyu, biyo bayan rikicin da ya ƙara ɓarkewa a ƙauyukan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wani ɓangare na sanarwar na cewa:
"Biyo bayan sake ɓarƙewar rikicin ƙabilanci tsakanin mutanen ƙauyukan Ilobu da Ifon, gwamnatin jihar Osun ta ba da umarnin dokar hana fita ta cigaba da aiki a ƙauyukan da lamarin ya shafa."
"Lokacin dokar hana fitan ya koma ƙarfe 6:00 na yamma zuwa ƙarfe 6:00 na safe. Za a taƙaita zirga-zirgar mutane da ababen hawa yayin dokar har sai an samu sabuwar sanarwa."
"Hakan wajibi ne domin daƙile yunƙurin lalata rayuka da dukiyoyi a cikin wannan lokacin, saboda rikicin filaye."
"Duk wanda aka kama yana yawo a ƙananan hukumomin Irepodun da Orolu a lokacin dokar hana fitan, za a cafke shi tare da fuskantar hukunci."
Gwaman Ottu Ya Sanya Dokar Kulle
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Cross Rivers, Bassey Ottu, ya sanya dokar hana fita a wasu ƙauyuka na jihar.
Gwamnan ya sanya dokar kullen ne a ƙauyukan Ugaga, Igbekurekor, Benekaba da Ijama na ƙaramar hukumar Yala ta jihar, biyo bayan ɓarkewar rikici.
Asali: Legit.ng