An Farfado Da Balarabe Abbas Bayan Ya Kife a Majalisar Dattawa

An Farfado Da Balarabe Abbas Bayan Ya Kife a Majalisar Dattawa

  • Jami'an lafiya da ke a majalisar dattawa sun samu nasarar farfaɗo da Balarabe Abbas Lawal bayan ya kife lokacin da ake tantance shi
  • Balarabe wanda Shugaba Bola Tinubu ya zaɓo domin zama minista daga jihar Kaduna, ya firgita jama'a bayan ya kife a zauren majalisar
  • Sai dai, an samu an farfaɗo da shi sannan aka fitar da shi daga zauren majalisar, yayin da majalisar ta cigaba da tantance ragowar sabbin ministocin

FCT Abuja - An farfaɗo da Balarabe Abbas Lawal, wanda Shugaba Tinubu ya zaɓo daga jihar Kaduna domin zama minista, bayan ya faɗi a lokacin da ake tantance shi a majalisar dattawa.

Balarabe ya faɗi ƙasa bayan ya yi magana na kusan mintuna 15, jami’an lafiya da aka kira zuwa cikin zauren majalisar ne dai suka farfaɗo da shi bayan ya faɗi.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Majalisar Dattawa Ta Tabbatar Da Zababben Ministan Da Ya Yanke Jiki Ya Fadi Da Wasu 2

Abbas Balarabe ya farfado bayan ya kife a majalisa
An samu nasarar farfado da Abbas Balarabe bayan ya kife a majalisa
Asali: UGC

Menene ya haddasa faɗuwar Balarabe?

Jaridar Channels tv ta ce wata majiya a majalisar dattawa ta bayyana cewa Balarabe yana fama da gajiya ne.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majalisar dattawa ta shiga wani zama na sirri ne a yayin da ake kokarin farfado da shi a cikin zauren majalisar.

Bayan an farfaɗo da shi, an fitar da shi daga zauren majalisar dattawa da motar ɗaukar marasa lafiya.

Majalisa ta cigaba da aikin tantancewa

Majalisar ta cigaba da tantancewar inda ta ɗora daga kan mutum na uku, Ayodele Olawande, wanda ya fito daga jihar Ondo.

Lawal na daya daga cikin sabbin ministoci uku da majalisar dattawar za ta tantance, inda sauran suka haɗa da Dr. Jamila Bio Ibrahim daga jihar Kwara da Ayodele Olawande daga jihar Ondo.

Balarabe shi ne mutum na biyu da aka tantance bayan shugaban majalisar dattawa, Sanata Opeyemi Bamidele, ya gabatar da kudirin tsawaita zaman majalisar fiye da 2:00 na rana domin kammala ayyukan majalisar na ranar.

Kara karanta wannan

Gwamna Ya Maida Ma'aikata Sama da 700 da Gwamnati Ta Kora Daga Aiki, Zai Biyasu Albashi Tun 2018

Tinubu Ya Maye Gurbin El-Rufai Da Balarabe Lawal

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya zaɓo sakataren gwamnatin jihar Kaduna, Balarabe Abbas Lawal, domin zama minista a gwamnatinsa.

Balarabe wanda na kusa da tsohon gwamnan jihar Kaduna ne, Malam Nasir El-Rufai, shi ne zai maye gurbin tsohon gwamnan a matsayin minista daga jihar Kaduna, bayan majalisa ta ƙi amincewa da shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng