Dan Majalisar Tarayya, Abdullahi Balarabe, Ya Bukaci A Ba Mutane Damar Kare Kansu

Dan Majalisar Tarayya, Abdullahi Balarabe, Ya Bukaci A Ba Mutane Damar Kare Kansu

  • Ɗan majalisar Bakori da Danja a zauren Majalisar Wakilai, Abdullahi Balarabe Dabai ya bayyana yadda za a magance matsalolin tsaro
  • Honorabul A. B Dabai ya bukaci gwamnati ta bai wa al'umma damar kare kawunansu ta hanyar sanya idanun jami'an tsaro
  • Hadimin Ɗan majalisar ya yi wa wakilin Legit Hausa ƙarin haske dangane da wannan kudiri na haɗin guiwa

FCT Abuja - Ɗan majalisa mai wakiltar Bakori da Danja a zauren Majalisar Wakilai, Abdullahi Balarabe Dabai, ya buƙaci a bai wa al'ummar yankin damar kare kawunansu daga hare-haren 'yan ta'adda.

Honorabul Abdullahi Dabai ya roƙi a ɗauki matakin bai wa kowa damar kare kansa ta hanyar kulawa da sa idon jami'an tsaron Najeriya.

Dan Majalisar Bakori da Ɗanja, Abdullahi Balarabe Dabai.
Dan Majalisar Tarayya Daga Katsina Ya Bukaci A Ba Mutane Damar Kare Kansu Hoto: Abdullahi Balarabe Dabai
Asali: Facebook

Ya bayyana hakan ne a zauren majalisar, a zaman da ta yi na ranar Talata, 03 ga watan Oktoba kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Mummunan Ibtila'i Ya Laƙume Rayukan Mutum 6 a Babban Titin Kaduna Zuwa Abuja

An buƙaci a ajiye sojojin a yankin da matsalar tsaro ta yi ƙamari

Abdullahi Dabai ya kuma buƙaci a kai barikin soji a mazaɓarsa ta Bakori-Danja da ke jihar Katsina, wacce take fama da yawaitar hare-haren 'yan bindiga.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kuma bukaci a ajiye sojojin a wasu yankuna na mazaɓar ta sa da suka fi fuskantar hare-haren masu garkuwa da mutane a cikin 'yan kwanakin nan.

A jawabin da ya gabatar yayin miƙa kudirin na haɗin guiwa, Ɗan majalisar ya ce:

"Ina alfaharin miƙa kudirin kafa 'yan sandan yanki ta yadda mutane zasu samu damar ɗaukar makami su kare kansu ta hanyar kulawar jami'an tsaro."
"Haka kuma ina roƙon a girke dakarun sojoji a Guga, Kakumi da Kandarawa da ke ƙaramar hukumar Bakori da kuma kafa sansanin sojoji a mazaɓar Bakori da Ɗanja."

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa Ya Fara Tono Badaƙalar Tsohon Gwamna, Sakataren PDP Ya Maida Mota

Ƙudurin da ya gabatar ya samu karɓuwa a gaban majalisar, inda ya ba da tabbacin cewa za a yi duk abinda ya dace wajen tabbatar da samuwar tsaro a yankin da ma ƙasar baki ɗaya.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da al'ummar Najeriya musamman ma dai na yankin Arewacin Najeriya ke ƙara kokawa kan ƙaruwar hare-haren yan bindiga a yankunansu.

Legit.ng Hausa ta tuntuɓi mai baiwa ɗan majalisar shawara ta musamman, Anas Jobe Aliyu, wanda ya ce asalin kudirin na haɗin guiwa ne daga yan majalisar Arewa ta Yamma.

Joɓe ya faɗa wa wakilinmu cewa mutane sun nuna farin ciki matuƙa kan wannan kudiri duba da halin da yankin ke ciki na ƙalubalen tsaro.

"Eh tabbas mai gida ya kai kudiri amma na haɗin guiwa, baki ɗaya yan majalisar wakilan shiyyar Arewa maso Yamma ne suka haɗu suka miƙa kudirin kuma ya karbu."
"Idan ka duba halin da arewa ke ciki ba sai nace maka komai ba, muna buƙatar gwamnati ta tashi tsaye kan rashin tsaro. Mai gida ya nemi a karfafa jama'a su riƙa kare kansu."

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP Ya Kai Ziyara Ta Musamman Jami'ar Tarayya Ta Gusau Kan Ɗaliban da Aka Sace

"Ya nemi a kawo sansanin sojoji mazaɓar mu ta Bakori da Ɗanja, kuma a tura sojoji wasu ƙauyuka uku saboda taɓarɓarewar tsaro, muna fatan a yi abinda ya dace.

Kano: Gwamnatin Abba Gida-Gida Ta Bada Hukun Kwana Daya Na Maulidi

A wani labarin na daban Abba Gida-Gida ya ayyana ranar Laraba, 4 ga watan Oktoba, 2023 a matsayin ranar hutun Maulidin Annabi Muhammad SAW.

Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano, Malam Baba Dantiye, ya ce Gwamnan ya roƙi mutane su yi koyi da halayen Annabi a rayuwarsu ta yau da kullum.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262