Kano: Gwamnatin Abba Gida-Gida Ta Bada Hutun Kwana Daya Na Maulidi

Kano: Gwamnatin Abba Gida-Gida Ta Bada Hutun Kwana Daya Na Maulidi

  • Abba Gida-Gida ya ayyana ranar Laraba, 4 ga watan Oktoba, 2023 a matsayin ranar hutun Maulidin Annabi Muhammad SAW
  • Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano, Malam Baba Dantiye, ya ce Gwamnan ya roƙi mutane su yi koyi da halayen Annabi a rayuwarsu
  • Malamin makaranta, Sanusi Isiyaku, ya faɗa wa wakilin mu cewa wannan ne karo na farko da gwamnatin Kano ta bada hutun

Jihar Kano - Gwamna Abba Kabir Yusuf wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida na jihar Kano ya ba da hutun kwana ɗaya a matsayin hutun Maulidin bana 2023.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Abba Gida-Gida ya ayyana ranar Laraba, 4 ga watan Oktoba, 2023 a matsayin ranar hutu domin murnar haihuwar fiyayyen halitta Annabi Muhammad SAW.

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf.
Kano: Gwamnatin Abba Gida-Gida Ta Bada Hukun Kwana Daya Na Maulidi Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Twitter

Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida na jihar Kano, Malam Baba Dantiye, ya fitar ranar Laraba a birnin Kano.

Kara karanta wannan

Gwamnan Benue Ya Bayyana Adadin Kudin Fansan Da Aka Biya Kafin Sakin Kwamishinansa Da Aka Sace

Gwamnan Kano ya ja hankalin 'yan Najeriya

Dantiye ya ce gwamnan ya bukaci jama’a da su yi amfani da wannan damar wajen yin koyi da halayen Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka zalika Gwamna Abba Gida-Gida ya roƙi ɗaukacin mazauna Kano da su dauki koyarwar Annabin rahama su sanya cikin harkokinsu na yau da kullum.

Kwamishinan ya ƙara da cewa Abba ya kuma bukaci mutane su dage da yin addu’a domin samun zaman lafiya da ci gaba a jihar Kano da ma Najeriya baki daya, kamar yadda Pulse ta ruwaito.

“Muna addu’ar Allah ya bamu ikon tsallake wannan mawuyacin lokaci kuma ya albarkace mu a cikin wannan damina da kuma lokacin noman rani mai zuwa,” in ji shi.

Wannan hutu da gwamnatin Kano ta bayar na zuwa ne mako ɗaya bayan hutun da gwamnatin tarayya ta bayar na bikin watan Maulidi da wasu Musulmai ke gudanarwa.

Kara karanta wannan

Jerin Sunaye: Abba Gida-Gida Ya Naɗa Sabbin Shugabanni 10 a Hukumomin Gwamnatin Kano

A wannan wata na Rabi'ul Awwal ne aka haifi fiyayyen halitta, Annabi Muhammad (Tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi).

Wani malamin makaranta a cikin birnin Kano, Sanusi Isiyaku, ya faɗa wa Legit Hausa cewa ba a taɓa bada wannan hutun ba a Kano sai a lokacin mulkin NNPP.

Malam Isiyaku ya ce duk da sanarwam hutun ta fito a makare mutane sun ji daɗi sosai, domin sun yi bikin Takutaha, wani Maulidi da ake yi a Kano cikin farin ciki.

"A makare sanarwan tazo domin wasu har sun tafi kai yaransu makaranta saboda ba a taɓa bada hutun Takutaha ba a Kano. Shi Takutaha wani Maulidi ne da ake yi a wuri ɗaya, wasu kuma na zagaye."
"Yana da banbanci a asalin hutun Maulidi da gwamnati ta saba bayarwa, bana ne kaɗai aka taɓa bada hutun wannan rana, kuma abun ya yi jama'a daɗi."

Sanatoci Sun Tsige Shugaban Majalisar Dattawa Daga Muƙaminsa Kan Abu 1? Gaskiya Ta Bayyana

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Hatsabibin Dan Ta'addan Da Ke Yawan Kashe Jama'a Ya Gamu da Ajalinsa a Jihar Arewa

Kuna da labarin Wasu rahotanni a soshiyal midiya sun yi iƙirarin cewa an tsige Sanata Godswill Akpabio daga matsayin shugaban majaisar dattawa.

A binciken da aka gudanar kan batun tsige Sanata Akpabio an gano cewa ba gaskiya bane, ya kamata mutane su guji rahoton da ke yawo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262