Yan Sanda Sun Cafke Naira Marley Kan Mutuwar Mohbad

Yan Sanda Sun Cafke Naira Marley Kan Mutuwar Mohbad

  • Rundunar ƴan sanda a jihar Legas, sun yi caraf da fitaccen mawaƙin nan Azeez Fashola, wanda aka fi sani da Naira Marley
  • An kama Naira Marley ne domin yi masa tambayoyi kan mutuwar tsohon yaronsa, Ilerioluwa Aloba, wanda aka fi sani da Mohbad
  • Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan jihar Legas SP Benjamin Hundeyin ya tabbatar da aukuwar hakan a shafinsa na X, a ranar Talata, 3 ga watan Oktoba

Ikeja, jihar Legas - An cafke Azeez Fashola, wanda aka fi sani da Naira Marley, domin yi masa tambayoyi da sauran bincike dangane da mutuwar Mohbad.

Hakan ya fito ne daga bakin Benjamin Hundeyin, jami'in hulda da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar Legas.

Yan sanda sun cafke Naira Marley kan mutuwar Mohbad
Yan sanda sun yi wa Naira Marley tambayoyi kan mutuwar Mohbad Hoto: Naira Marley, Mohbad
Asali: Facebook

Hundeyin ya tabbatar da hakan ne cikin wata sanarwa a shafinsa na X (wanda a baya aka fi sani da Twitter) a ranar Talata, 3 ga watan Octoban 2023.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Kai Farmaki a Jami'ar Usmanu DanFodiyo? VC Ya Yi Karin Haske

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mohbad: "Na dawo", Naira Marley

Tun da farko, Naira Marley ya wallafa a shafinsa na X cewa ya dawo gida Najeriya. Mawaƙin ya kuma ce zai gana da jami'an ƴan sanda.

A kalamansa:

"Ina so in bayyana cewa na dawo Legas, Najeriya don taimakawa hukumomi kan binciken da ake yi, yana da muhimmanci yi hakan ga Imole, zan gana da ƴan sanda tare da fatan gaskiya za ta bayyana kuma za a yi adalci."

Mutuwar Mohbad ta bar baya da ƙura

Mutuwar mawaƙi Ilerioluwa Aloba wanda aka fi sani da Mohbad ta bar baya da ƙura saboda yadda ƴan Najeriya suka yi ta magana kan mutuwarsa.

Wasu da dama na ganin cewa mawaƙin ya bar duniya ne bisa halin ƙuncin da rayuwarsa ta shiga tun bayan da ya samu saɓani da tsohon ubangidansa Naira Marley.

Kara karanta wannan

Faston Najeriya Fabian Nna Ya Tayar Da Matacce? Gaskiya Ta Bayyana

Mutane da dama sun yi ta kira kan ƴan sanda da su cafke Naira Marley saboda suna zargin da sa hannunsa a mutuwar Mohbad, zargin da mawaƙin ya fito ya musanta.

Ƴan sanda sun tono gawar Mohbad

A wani labarin kuma, rundunar ƴan sandan jihar Legas da wasu ma'aikata lafiya sun haƙo gawar Mohbad daga cikin kabari.

Jami'an ƴan sanda sun tono gawar ne domin gudanar da bincike kan musabbabin mutuwar mawaƙin wanda ya bar duniya a ranar 12 ga watan Satumba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng