Borno: ISWAP Ta Bindige Kwamandan Boko Haram Har Lahira a Dajin Sambisa

Borno: ISWAP Ta Bindige Kwamandan Boko Haram Har Lahira a Dajin Sambisa

  • Mayakan ƙungiyar ta'addanci ISWAP sun harbe wani babban kwamandan 'yan Boko Haram, Ali Gana Alhaji Ali har lahira a dajin Sambisa
  • Kwamandan yana ɗaya daga cikin hatsabiban 'yan ta'addan da suka hana mutane zaman lafiya a hanyoyi da dama a jihar Borno
  • Wannan ba shi ne karo na farko da ake samun arangama tsakanin ƙungiyoyin 'yan ta'addan biyu masu adawa da juna ba

Jihar Borno - Mayakan kungiyar ta'addancin ISWAP sun halaka kwamandan kungiyar Boko Haram mai kula da sansanonin Sambisa da Gwoza, Ali Gana Alhaji Ali, a jihar Borno.

Wata majiya ta shaida wa Daily Trust cewa, an kashe Ali, daya daga jagororin ‘yan ta’addan da suka fi hatsari a Borno, a wani harin kwantan bauna da mayakan ISWAP suka kai ranar Lahadi.

Taswirar jihar Borno.
Borno: ISWAP Ta Bindige Kwamandan Boko Haram Har Lahira a Dajin Sambisa Hoto: dailytrust
Asali: UGC
“Shi ne mataimakin marigayi Ali Ngulde, kuma idan aka cire Shekau, babu wanda ya kashe mutane da yawa kamar sa daga dajin Sambisa har zuwa Bayan Dutsen Gwoza."

Kara karanta wannan

Dan Kasuwa A Kano, Dantata Ya Kirkiro Bankin Yanar Gizo Da Zai Yi Gogayya Da Opay, Kuda, Ya Dauki Alkawari

"Shi kasurgumin makashi ne, har 'yanzu mayakansa sun hana jama'a zaman lafiya tare da sa fargaba ga ƙauyuka, manoma da matafiya a yankunan Pulka, Bankin, Bama da Gwoza Mubi."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Ba su kama mutane su tsare, ana yanka mutane a gonakinsu a kowane mako. Babu shakka mutanen Gwoza za su yi murnar rasuwarsa,” inji majiyar.

Yadda ISWAP da Boko Haram ke yaƙar juna

Wannan dai na zuwa ne sama da shekaru biyu bayan shugaban 'yan ta'addan Boko Haram, Abubakar Shekau, ya tarwatsa kansa a wani kazamin artabu da mayakan na ISWAP a watan Mayun 2021.

A makon da ya gabata, dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Goza, Damboa da Chibok a majalisar wakilai ta kasa, Usman Ahmed Jaha, ya yi tir da kisan manoma 10 a cikin kwanaki 10 a yankin Goza.

Ya kuma koka kan yadda ake kashe manoma a kullum kwana a yankin domin tsoratar da su daga girbin amfanin gonakinsu, kamar yadda Daily Post ta rahoto.

Kara karanta wannan

Babu Wata Yarjejeniya Da Emefiele Kan Dawo da ‘Biliyan 50’, Gwamnatin Tinubu

An Samu Asarar Rai a Wani Hatsarin Mota a Hanyar Legas-Ibadan

A wani rahoton na daban Wani mummunan hatsarin mota ya ritsa da mutane masu yawa a kan titin hanyar Legas zuwa Ibadan.

Mutum ɗaya ya riga mu gidan gaskiya yayin da wasu fasinjoji bakwai suka samu raunika a harin da ya auku a tashar motar Magboro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262