Farashin Gas Ya Kai N1,000 Kan Kowace kg, Yan Najeriya Sun Koka

Farashin Gas Ya Kai N1,000 Kan Kowace kg, Yan Najeriya Sun Koka

  • Yan Najeriya sun ce ba su ji dadin yadda farashin gas din girki ke ci gaba da tashin gwauron zabi ba
  • Hakan ya kasance ne yayin da farashin gas ya kai kimanin N1,000 a wasu yankunan kasar
  • Sun ce lamarin babu adalci a ciki duba ga matsin tattalin arziki da ake ciki a kasar yanzu haka

Yan Najeriya sun nuna rashin jin dadi da tashin farashin gas din girki, wanda aka ce ya kai kimanin N1,000 kan kowace kg.

Wadanda suka siya gas a baya-bayan nan sun fada ma jaridar Legit cewa basu ji dadin karin kudin gas da aka yi ba da yadda ake ci gaba da wahala a Najeriya.

Farashin gas ya yi tashin gwauron zabi
Farashin Gas Ya Kai N1,000 Kan Kowace kg, Yan Najeriya Sun Koka Hoto: Pulse Nigeria
Asali: UGC

Olatunbosun Oladapo, shugaban kungiyar yan kasuwar fetur da gas (NALPGM), ya bayyana cewa farashin cika tukunyar gas 12.5kg yana shirin tashi zuwa N18,000 zuwa Disambar 2023.

Kara karanta wannan

Yan Najeriya Na Cikin Jalala Yayin Da Gas Mai Nauyin Kilo 12 Ya Kai N12,500, An Yi Hasashen Abin Da Zai Faru

Farashin gas ya karu

Hauwa Muhammed, wacce ke zama a Olodi-Apapa, ta fada ma Legit cewa ta cika da mamaki da jin sabon farashin na N1,000 a lokacin da ta je gidan mai. Bata yi tsammanin farashin ya kai haka ba daga lokacin da ta siya na karshen.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta ce:

"Yan kwanaki da suka gabata, na siya N800 kan kowace lita kawai sai na naji yanzu ya kai N1,000 kowace kg. Wannan ya yi mana yawa da za mu iya jurewa. Ba ma iya girki cikin kwanciyar hankali."

Muhammed ta ce ta yanke shawarar siyan 4KG saboda kudin da ta ware na siyan 6KG ba zai iya ba.

Israel Sunday ya nuna fusata kan ci gaban. A cewarsa, ya siya kg din gas kan N700 a watan jiya. Ya bayyana cewa idan haka ya ci gaba, toh gas zai zama na masu hannu da shuni kadai.

Kara karanta wannan

Yajin-Aiki: Tinubu Ya Karawa Ma’aikata N10, 000 a Yunkurin Lallabar ‘Yan Kwadago

Hajara Musa ta ce ita ta yanke shawarar komawa ga gawayi saboda gas ya fara fin karfinta.

Ta ce:

"Abun sai dai mu ce Innalillahi wa'inna ilaihi rajiun. Talaka ya ga ta kansa a wannan hali da ake ciki yanzu. Ni na fara hakura da gas ina dan hadawa da gawayi amma na kusa komawa gawayi gaba daya."

Asiya Jamil kuwa cewa ta yi yan Najeriya na cikin halin wayyo Allah domin a cewarta ana kokarin sabawa da tsadar rayuwa da ake ciki sai ga wani lamari na kara kunno kai.

Tallafi ya dawo bayan Tinubu ya biya N169b a Agusta don tsayar da farashin lita a N620

A wani labarin, mun ji cewa Gwamnatin Shugaban kasa Bola Tinubu ta biya Naira biliyan 169.4 na tallafin mai a watan Agusta.

Gwamnatin ta biya kudin tallafin ne domin tabbatar da cewa farashin litar mai ta tsaya a kan Naira 620 ba tare da ta yi sama ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng