Yan Bindiga Sun Sace Mutum 19 a Wani Sabon Hari a Jihar Kaduna
- Ƴan bindiga sun kai sabon farmaki a ƙauyen Angwanwaku cikin masarautar Kufana a ƙaramar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna
- Miyagun ƴan bindigan sun halaka mutum ɗaya tare da yin awon gaba da wasu mutum 19 a harin da suka kai
- Gwamnatin jihar da rundunar ƴan sandan jihar dai ba su ce komai ba dangane da wannan sabon harin da aka kai a daren ranar Asabar
Jihar Kaduna - Wasu ƴan bindiga sun kai farmaki a ƙauyen Angwanwaku da ke masarautar Kufana a ƙaramar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna.
Ƴan bindigan a yayin harin sun halaka mutum ɗaya tare da yin awon gaba da aƙalla mutum 19 ciki har da mata da ƙananan yara, cewar rahoton The Punch.
Yadda harin ya auku
Sakataren masarautar Kufana, Tanimu Makaddas, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 12:00 na daren ranar Asabar, 30 ga watan Satumba, lokacin da maharan suka dira a ƙauyen, rahoton Vanguard ya tabbatar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sakataren ya bayyana sunayen waɗanda abin ya shafa, inda ya ce an kashe Kukah Yari, tare da raunata Abuki Dogo a yayin harin.
Sai dai, Makaddas ya bayyana cewa waɗanda aka sace ɗin sun haɗa da, Yakubu Abba, Basiru Maiwada, Keziya Silas, Peace Silas, Lami Istifanus, Habila Musa, Bege Liazarus, Joshua Abuki, Juliana Habila, Stella Yohanna.
Sauran ya ce, su ne Farawa Ezikiel, Deborah Ezikiel, Salomi Dutse, Rifkatu Zaphaniah, Tamar Liazarus, Ejah Habila, Rejoice Ezikeil, Catharine Sila, da Gundu Rubu.
Me hukumomi suka ce dangane da harin?
Babu wata sanarwa a hukumance dangane da faruwar lamarin ko dai daga ‘yan sanda ko kuma gwamnatin jihar.
Har ya zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton, muƙaddashin kakakin rundunar ƴan sandan jihar, Mansir Hassan, bai ce komai ba kan tuntuɓarsa da aka yi dangane da lamarin.
Mahaifiya Ta Cafke Wanda Ya Sace Yarta
A wani labarin na daban kuma, wata mata ta samu nasarar cafke wani mugun ɗan ta'adda da ya sace ƴarta tare da halaka a garin Zariya da ke jihar Kaduna.
Matar dai ta samu nasarar cafƙe ɗan ta'addan ne lokacin da aka je kai masa kuɗaɗen fansan da ya nemi a ƙara masa kafin ya sako yarinyar duk da cewa ya halaka ta.
Asali: Legit.ng