Shugaba Tinubu Zai Rabawa Talakawa Miliyan 15 a Najeriya Kudade Daga Watan Oktoba

Shugaba Tinubu Zai Rabawa Talakawa Miliyan 15 a Najeriya Kudade Daga Watan Oktoba

  • Shugaban kasa Tinubu ya bayyana shirin fara rabon kudi ga talakawa a Najeriya don rage radadin talauci da ake ciki
  • Ya kuma bayyana matsayar gwamnatinsa wajen yaki da ta’addanci tare da kokarin wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali
  • Legit Hausa ta ji shugaban na cewa, zai ci gaba da nade-nade daidai da tsarin dimokradiyya da kundin tsarin mulkin kasa

FCT, Abuja - Shugaba Bola Tinubu a ranar Lahadin ya ce gwamnatinsa za ta fara aikin turawa talakawa miliyan 15 kudade farawa daga watan Oktoba.

Shugaban ya bayyana haka ne a jawabinsa na murnar zagayowar ranar samun ‘yancin kai na farko a matsayin shugaban kasa, inda ya yi alkawarin bunkasa ayyukan yi da kuma kudaden shiga a birane.

A jawabinsa da wakilin Legit Hausa ya gani, shugaban ya ce, gwamnatinsa za ta karfafa bunkasa kananan ‘yan kasuwa da kuma samar da ayyukan yi ga matasa.

Kara karanta wannan

Dole za ku sha wahala: Tinubu ya ce 'yan Najeriya su shirya shan kebura, gyara babu dadi

Shugaba Tinubu zai raba kudi ga talakawa
Tinubu zai ragewa talakawa radadi | Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Magance matsalar tsaro a Najeriya

Dangane da batun tsaro, shugaban ya kuma jaddada kudirin gwamnatinsa na kare rayuka da dukiyoyin ‘yan Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A hakan, shugaban kuma babban kwamanda tsaron kasa ya ce hukumomin tsaro za su kara karfafa hadin kai tsakaninsu da tattara bayanan sirri don magance matsaloli.

A cewar Tinubu, ya dora wa manyan hafsoshin tsaro alhakin sake gina ginshikin karfin aiki ga jami’an tsaron kasar nan.

Yabon Tinubu ga masu ruwa da tsaki

Shuagban ya kuma yabawa kotun kasar nan bisa tabbatar da aiki kan doron dimokradiyya da kuma jajircewa wajen tabbatar da gaskiya.

A bangare guda, ya yabawa majalisun kasar nan bisa ba shi hadin kai wajen tabbatar da nade-nadensa masu ma’ana.

Daga karshe, ya bayyana aniyarsa na ci gaba da yin nade-naden da suka dace don kawo ci gaba ga Najeriya da ‘ya’yanta.

Kara karanta wannan

Dama-dama: Tinubu ya karawa ma'aikata albashi, amma akwai abin kura a gaba

Za a sha wahala kafin gyara kasa, inji Tinubu

A bangare guda, shugaba Bola Tinubu ya ce akwai bukatar ‘yan Najeriya su jure wa kalubalen wahalar tattalin arziki da ake fama da shi a kasar nan domin samun ingantacciyar makoma.

A jawabin da ya yi na bikin cikar Najeriya shekaru 63 da samun ‘yancin kai a ranar Lahadi, Tinubu ya ce gyare-gyaren da ya sa a gaba za su ba da wahala amma gwamnatinsa na yin duk mai yiwuwa don kyautata rayuwar ‘yan kasa.

Shugaban ya ce sauye-sauyen tattalin arzikin da gwamnatinsa ta bullo da shi zai dora al'ummar kasar kan turbar wadata da ci gaba a nan gaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.